ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Yi Watsi Da Wannan “Mummunan Teburi”

by Sulaiman
3 months ago

Da jimla daya za a iya takaita salon jagorantar harkokin duniya na kasashen yamma, wato maganar da tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Antony Blinken, ya fada, wadda ta kasance kamar haka: “A tsarin kasa da kasa, idan ba ka zauna a gefen teburin cin abinci ba, to, za ka zama cikin takardar oda. “Idan an bari kasashen yamma sun ci gaba da jagorantar harkokin duniya, to, za a ga yadda suke rikida karin kasashe masu tasowa zuwa “abincin dake cikin takardar oda”. Kuma dimbin abubuwan da suka auku a shekarun baya sun shaida gaskiyar hakan. Misali, rikice-rikicen da kasashen yamma suka tayar da su a yankuna daban daban sun haddasa tsaiko ga tsarin samar da kayayyaki, lamarin da ya sanya kasashen Afirka fuskantar mummunar matsalar hauhawar farashin kayayyaki, inda aka yi hasashen cewa, matsakaicin adadin hauhawar farashin kayayyaki a nahiyar Afirka a shekarar 2026 zai kai kaso 10.4%.

Haka zalika, manyan hukumomin tantance yanayin da ake ciki a fannin hada-hadar kudi, da kasashen yamma ke jan ragamarsu, sun kambama hadarin da masu zuba jari ke iya fuskanta a nahiyar Afirka, ta yadda suka raunana karfin kasashen Afirka na janyo jari, da kara musu wuya ta fuskar neman samun lamuni.

Kusan duk wata manufar da kasashen yamma suka fitar, ta kan zama mai lahanta moriyar kasashe masu tasowa. Saboda haka, lokaci ya yi da za a jefa “teburin cin abinci” na kasashen yamma mai salon “kashin dankali” cikin kwandon shara.

ADVERTISEMENT

To, hakan shi ne dalilin da ya sa kasar Sin ke ba da shawara ga kasashen duniya, don a gina wani tsarin jagorantar harkokin duniya mai nuna adalci da sanin-ya-kamata. A watan Satumban bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta tsarin jagorantar harkokin duniya, wadda ta jaddada muhimmancin wasu ka’idoji 5, wato tabbatar da daidaiton ikon mulkin kai na kasashe daban daban, da kula da harkokin kasa da kasa bisa doka, da sanya bangarori daban daban cudanya da hadin kai tsakaninsu, da dora moriyar jama’a a kan sauran harkoki, da daukar takamaiman matakai masu amfani.

Sa’an nan a jiya, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da takardar bayani mai alaka da aikin jagorantar harkokin duniya, wadda ta bayyana matakan da kasar Sin ta dauka a kokarin aiwatar da shawarar inganta tsarin jagorantar harkokin duniya.

LABARAI MASU NASABA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Tunanin kasar Sin game da tsarin jagorantar harkokin duniya, wanda ya dora muhimmanci kan adalci maimakon karfi da iko, ya samu karbuwa daga dimbin kasashe masu tasowa. Kana bayan da kasar ta gabatar da shawarar jagorantar harkokin duniya, nan take ta samu goyon baya daga kimanin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 160, ciki har da tarayyar Najeriya.

Masana da ‘yan jarida da yawa daga kasashen Afirka ma sun amince da shawarar da kasar Sin ta bayar kan inganta tsarin jagorantar harkokin duniya. Inda shahararren dan jarida a Najeriya Lawal Sale, ya rubuta a cikin wani sharhinsa cewa, “Wannan shawara za ta haifar da karin kwanciyar hankali, da yanayi na tabbas a duniyarmu mai cike da tashin hankali, musamman ma a nahiyar Afirka.” Kana a nasa bangare, Paul Frimpong, wani shehun malami dan kasar Ghana, ya ce shawarar nan “tana tabbatar da cewa tsarin jagorancin duniya ba zai ci gaba da zama karkashin mallakar wasu kasashe masu karfi ba.” Kana dan jaridar kasar Lesotho, Silence Charumbira, ya ce shirin na baiwa kananan kasashe damar zama masu hakikanin ‘yancin kai.

A nasa bangare, Saxon Zvina, shahararren marubuci dan kasar Zimbabwe, ya bayyana cikin wata makalarsa cewa, ko da yake an gabatar da shawarar inganta tsarin jagorantar harkokin duniya bisa nagartacciyar niyyar gina tsarin duniya mai nuna adalci da sanin-ya-kamata, amma yunkurin cika wannan burin da aka sanya na fuskantar kalubale, ganin yadda bangarorin da suka amfana daga tsarin jagorancin duniya na yanzu za su ki yarda da gudanar da gyare-gyare, kana tsanantar takarar siyasa ita ma tana haifar da cikas ga yunkurin kawo sauye-sauye.

Ko za a iya daidaita tsarin jagorancin duniya cikin nasara, ko kuma akasin haka, ya danganta da niyyar gamayyar kasa da kasa ta daukar mataki cikin hadin gwiwa. Idan ba a son sake ganin wannan mummunan “teburi” na mai da kasashe marasa karfi a matsayin “abinci”, to, yanzu lokaci ya yi na yin kokari tare don jefa “teburin” cikin kwandon shara. (Bello Wang)

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sultan Ya Gargaɗi Malaman Addini Kan Kare Masu Cin Hanci Da Rashawa
  • Sulaiman
    ’Yansanda Sun Ƙwato Motoci 52, Sun Kama Masu Laifi 177 A Mako Guda
  • Sulaiman
    Kada Ku Ɗauki Nauyin Aikin Hajji Da Kuɗaɗen Da Aka Sace — Sultan Ga ’Yan Siyasa
  • Sulaiman
    Ya Kamata Kowane Dan Nijeriya Ya Samu Horon Soja – Ministan Tsaro

MASU ALAKA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka
Ra'ayi Riga

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

September 14, 2026
Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Next Post
Tinubu

Rashin Tsaro: CUPP Ta Goyi Bayan Kiran Da Aka Yi Wa Tinubu Na Jagoranci Ko Murabus

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Kyaftin Super Eagles William Troost-Ekong Ya Karɓi Musulunci A Qatar

Tsohon Kyaftin Super Eagles William Troost-Ekong Ya Karɓi Musulunci A Qatar

September 24, 2026
’Yan Bindiga Sun Sace Matafiya 28 A Jihar Filato

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sa-kai 3, Rami Ya Rufta Kan Masu Haƙar Ma’adinai 4 A Filato

September 24, 2026
Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

September 23, 2026
Zargin Maita: ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Huɗu Bisa Hallaka Wani A Bauchi

Zargin Maita: ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Huɗu Bisa Hallaka Wani A Bauchi

September 23, 2026
Dandalin Al’adu Na Beijing Zai Mayar Da Hankali Ga Batun Gadon Al’adu Da Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai

Dandalin Al’adu Na Beijing Zai Mayar Da Hankali Ga Batun Gadon Al’adu Da Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai

September 23, 2026
Sultan

Sultan Ya Gargaɗi Malaman Addini Kan Kare Masu Cin Hanci Da Rashawa

September 23, 2026
Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Nuna Kwarewar Sana’o’i Na Duniya Na Shekarar 2026

Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Nuna Kwarewar Sana’o’i Na Duniya Na Shekarar 2026

September 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Ƙwato Motoci 52, Sun Kama Masu Laifi 177 A Mako Guda

September 23, 2026
Yayin Da Taron UNGA Na 81 Ya Zo A Lokacin Da Duniya Ta Shiga Tsaka-mai-wuya…

Yayin Da Taron UNGA Na 81 Ya Zo A Lokacin Da Duniya Ta Shiga Tsaka-mai-wuya…

September 23, 2026
Sultan

Kada Ku Ɗauki Nauyin Aikin Hajji Da Kuɗaɗen Da Aka Sace — Sultan Ga ’Yan Siyasa

September 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.