ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Na Daukar hakikanan Matakan Gina Kyakkaywar Makomar Al’ummun Sin Da Afirka Ta Bai Daya

by CGTN Hausa and Sulaiman
3 months ago
Sin

A Bangaren Kiwon Lafiya Kwanan nan, babban darektan cibiyar kandagarkin cututtuka ta Afirka wato Africa CDC Dr. Jean Kaseya ya bayyana cewa, Sin ta ba da tallafi mai karfi wajen taimaka wa kasashen Afirka tinkarar cutar Ebola a wannan karo, a fannonin tura ma’aikatanta da samar da kayayyaki da sauransu. Sin babbar kawar kasashen Afirka ce, kuma cibiyar tana fatan kara karfafa hadin gwiwa da ita.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana cutar Ebola da ta barke a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Uganda a wannan karo, a matsayin “matsalar lafiya da ke bukatar daukin gaggawa daga kasashen duniya”. Duba da hakan, kungiyar kwararrun likitocin Sin ta tashi daga birnin Beijing da sanyin safiyar ranar 2 ga watan Yuni cikin gaggawa, don taimaka wa nahiyar Afirka wajen yaki da cutar Ebola, inda za su gudanar da ayyuka na tsawon watanni uku.

Yawan mace-macen masu kamuwa da Ebola ya kan kai kashi 30 zuwa 90, kuma cuta ce mai saurin yaduwa, lamarin da ya sa shawo kanta ya zama aiki mai wuya. A cikin irin wannan hali ne, kungiyar kwararrun likitoci na kasar Sin da ta samu umurni sai ta tashi nan da nan zuwa Kinshasa ba tare da bata lokaci ba, kuma sun je tare da kayayyakin kandagarki da ake matukar bukata.

ADVERTISEMENT

Wannan ba shi ne karo na farko da Sin ta ba da taimako irin haka ba. A shekara ta 2014, lokacin da cutar Ebola ta jefa Afirka cikin mawuyancin hali, duniya ta shiga tsoron cutar, kuma kasashe da yawa suka janye kungiyoyin likitocinsu da ke Afirka, amma kasar Sin a nata bangare ta tura kungiyar likitocinta zuwa yankin da cutar ta shafa don ba da taimako. Bayan barkewar cutar a bana, tawagar likitocin Sin ta 24 da ke aiki a Kongo Kinshasa, ta dauki matakan gaggawa nan take. Kamar yadda masanin cututtuka na Kongo Kinshasa Jean-Jacques Muyembe ya ce, “Sai a lokacin wahala ake gane aboki na gaske.”Abin lura shi ne, tallafin da Sin ta bayar na yaki da cutar a Afirka ba “taimako na gaggawa” ba ne kawai.

Jagoran kungiyar kwararrun likitocin da kasar Sin ta tura zuwa Congo Kinshasa a wannan karo Lu Ming ya bayyana cewa, manufarsu ita ce taimakawa yankin wajen inganta karfinsu na yaki da cutar Ebola da kuma kiwon lafiya. A Uganda, tawagar likitocin Sin ta 25 da ke kasar ta taimaka wa asibitin sada zumunta na Sin da Uganda wajen inganta tsarinsa na tantance cututtuka da kuma rarraba marasa lafiya, tare da more dabarun kasar Sin wajen hana yaduwar cututtuka.Tun lokacin da Sin ta aika tawagar likitocinta ta farko zuwa Aljeriya a shekara ta 1963 zuwa yanzu, kasar ta tura ma’aikatan lafiya sama da 26,000 zuwa kasashen Afirka 48, inda suka samar da jiyya ga marasa lafiya sama da miliyan 230.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

A halin yanzu, ma’aikatan lafiya 900 da ke cikin tawagogin likitoci 45 da Sin ta tura kasashen Afirka 44 suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Za a magance cutar Ebola wata rana, amma hadin gwiwar sha’anin kiwon lafiyar jama’a tsakanin Sin da Afirka ba za ta tsaya ba.

Daga tura kungiyoyin likitoci zuwa gina cibiyoyin magance cututtuka, daga koyar da fasaha zuwa horar da ma’aikata, abubuwan da Sin ke yi ba “samar da taimakon gaggawa” ba ne kadai, yana kuma taimaka wa Afirka wajen gina ingantaccen tsarin kiwon lafiyar jama’ar nahiyar. Kamar yadda mataimakin firaministan kasar Sin Liu Guozhong ya fada a taron koli na musamman kan yaki da cutar Ebola da aka gudanar ta bidiyo a baya-bayan nan: “Sin da Afirka na da makomar bai daya.” Hakan ya sa, Sin take daukar hakikanan ingantattun matakai don gina kyakkaywar makomar al’ummar Sin da Afirka ta bai daya a bangaren kiwon lafiya.(Marubuciya: MINA)

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Nijeriya Ta Karbi Ƴan Nijeriya 268 Da Suka Tsero Daga Afirka Ta Kudu

Nijeriya Ta Karbi Ƴan Nijeriya 268 Da Suka Tsero Daga Afirka Ta Kudu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.