Da safiyar ranar 26 ga watan nan da muke ciki, an samu abkuwar mummunan ibtila’in zabtarewar kasa a bangaren kasar Nepal mai makwabtaka da kasar Sin, lamarin da ya janyo babbar hasarar rayuka gami da bacewar wasu mutane da dama a gundumar Gyirong ta birnin Xigaze na jihar Xizang mai cin gashin kanta ta kasar Sin, wato yankin kan iyakokin Sin da Nepal.
A yau Lahadi kuma an yi wani taron manema labarai a Gyirong dangane da ibtila’in, inda aka bayyana cewa, bayan abkuwarsa, an dauki matakan shawo kansa ba tare da bata lokaci ba a Xizang, inda aka kafa babban sashin kula da ayyukan ba da agajin gaggawa gami da wani sashin kula da agajin gaggawa da ke can yankin da ibtila’in ya ritsa da shi.
Ma’aikatar kudi, da ma’aikatar shawo kan al’amuran ba-zata ta kasar Sin, sun ware kudin Sin Yuan miliyan 120, kana, kwamitin samar da ci gaba da yin gyare-gyare a gida na kasar ya ware Yuan miliyan 100, a wani kokari na tallafa wa ayyukan ba da agaji da ceto da kuma farfado da yankin da ibtila’in ya shafa. Kawo yanzu, an riga an tura ma’aikata 2141 na bangarori daban-daban domin bayar da agajin gaggawa a wurin, ciki har da na rundunar ’yantar da jama’ar kasar Sin, da ’yan sanda masu dauke da makamai, da tawagar ’yan kwana-kwana masu kai dauki da sauransu, gami da motocin agaji guda 269, hade da na’urorin kai dauki 3922.
Zuwa karfe 6 na yammacin ranar 29 ga watan muke ciki, yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon ibtila’in ya kai 16, yayin da wasu 546 suka bace. (Murtala Zhang)














