Rundunar ƴansandan Jihar Kaduna ta ce jami’anta sun gudanar da sumamen share fage tare da rusa wasu sansanonin ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Makarfi ta jihar.
Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce an gudanar da aikin ne a ranar 29 ga Agusta, 2026, tare da haɗin gwiwar jami’an Sa-kai na Jihar Kaduna (Kaduna State Vigilance Service), Makarfi. Ya ce jami’an sun samu nasarar kai sumame sansanonin ’yan bindiga ne bisa sahihan bayanan sirri da al’ummar yankin suka bayar.
A cewarsa, jami’an tsaron sun kai samame a wasu wuraren da ake zargin ’yan bindiga na fakewa a yankunan Durum da Danguzuri, har zuwa kan iyakar Jihar Kano. An kuma rusa gine-gine biyu da aka gano cewa ’yan bindigar na amfani da su wajen tsare mutanen da suka yi garkuwa da su a Rugar Mijin Goggo da Unguwar Maryamu da ke Danguzuri.
Rundunar ta ce sintiri na haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro na ci gaba da gudana a yankin domin hana ’yan bindigar damar sake kafa sansanoni ko gudanar da ayyukansu. Ta ƙara da cewa an dawo da zaman lafiya, kuma yankin na cikin kwanciyar hankali.
Kwamishinan ƴansandan jihar Kaduna, Rabiu Muhammad, ya yaba wa al’ummomin yankin bisa haɗin kai da jami’an tsaro, tare da jinjina wa jami’an da suka gudanar da aikin. Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kai farmaki kan ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka a faɗin jihar.














