Jirage mara matuka na shawagi a sama domin nazarin yanayi, yayin da tawagar ma’aikatan ceto ke tafe a kafa zuwa yankunan da ibtila’in zabtarewar laka ya fi shafa a kafar Gyirong da ke yankin Xizang mai cin gashin kansa, a kudu maso yammacin kasar Sin. Toshewar titunan da barazanar sake aukuwar wani ibtila’in na kara dagula aikin lalubo daruruwan mutanen da suka bata.
Sashen kula da agajin gaggawa na yankin Xizang ya ce zuwa karfe 1 na dare na jiya, an tabbatar da mutuwar mutane 7 da batan wasu 554 a Gyirong da ke kan iyakar Sin da Nepal.
A cewar ma’aikatar harkokin wajen Sin, kasashen Sin da Nepal na tuntubar juna a kai a kai kuma suna hadin gwiwa a kokarin bincike da ceto, tana mai cewa dukkan rayuka ba tare da la’akari da kasashensu ba, na da daraja a wajen Sinawa ma’aikatan ceto. Da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar 26 ga wata, zabtarewar laka ta auku a Nepal, wadda ta haifar da mace-mace da bacewar mutane a kafar Gyirong dake gundumar Gyirong ta birnin Shigatse da ke yankin Xizang na kasar Sin. A jiya Juma’a ne kuma masana daga cibiyar bincike ta Nepal sun yi wa wakilan kafar yada labarai ta CMG ta Sin bayanin cewa, rugujewar kankara daga kan tsauni a bangaren kasar Nepal ce ta haifar da ibtila’in.
Wakilan na CMG sun ga wani hoton tauraron dan adam da masanan na cbiyar bincike ta jami’ar Tribhuvan ta Nepal suka nazarta. A cewar masanan, wurin rugugewar kankarar yana bangaren kasar Nepal a kogin Donglin Tsangpo da ke kan iyakar Sin da Nepal. Sun kara da cewa, dama ruwan dake malala daga narkewar kankarar kan tsauni, na zuba ne a cikin kogin.
Sai dai a wannan karon, saboda rugujewar da ta auku kwatsam, ta haifar da mummunan tasiri cikin kankanin lokaci. Kankara masu girma dauke da laka da rairayi daga tsaunika sun malala kasa, inda suka haifar da illa sosai ga bangaren Sin da ke kusa da kafar Gyirong. Haka kuma ibtila’in ya shafi wasu bangarorin Nepal, baya ga wuraren da ke kusa da kafar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














