A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki a kasar Kyrgyzstan, gami da halartar taron koli na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ta shekarar 2026, za a fara nuna wani shirin bidiyo da kafar yada labarai ta CMG ta kasar Sin ta tsara mai taken “Tsoffin bayanai da Xi Jinping yake so” ta kafofin yada labarai na kasashe mambobin kungiyar SCO, da suka hada da Kyrgyzstan, da Belarus, da Kazakhstan, da Pakistan, da Rasha, da Tajikstan, da Uzbekistan, da Iran, da dai sauransu.
A lokacin da aka tsara shirin bidiyo na “Tsoffin bayanai da Xi Jinping yake so”, an fi dora muhimmanci kan fannonin raya tattalin arziki, da kirkiro sabbin fasahohi, da kare muhallin halittu, da tabbatar da ingancin rayuwar jama’a, da dai makamantansu, inda aka dauki dimbin tsoffin bayanai daga littattafai da tarihi na kasar Sin, da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya taba ambata cikin jawaban da ya yi, da rubutattun bayanansa, a kokarin nuna wa masu kallo na kasashe mambobin kungiyar SCO alakar dake tsakanin tunanin shugaba Xi Jinping ta fuskar gudanar da mulki da al’adu da tarihi na kasar Sin, da dabaru da fasahohin kasar wajen daidaita matsalolin dake damun al’ummun duniya. (Bello Wang)














