Ma’aikatan lafiya a Jihar Katsina sun sanar da fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki 7, sakamakon gazawar gwamnatin jihar wajen magance matsalolin da suka gabatar mata.
Ma’aikatan, waɗanda ke ƙarƙashin ƙungiyar “Assembly of Health Care Professionals in Katsina State”, sun sanar da fara yajin aikin ne a ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026, bayan ƙarewar wa’adin kwanaki 7 da suka bai wa gwamnatin jihar domin biyan buƙatunsu.
Da yake yi wa manema labarai bayani, shugaban ƙungiyar, Comrade Ibrahim Balange, ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren Laraba.
Ya bayyana cewa ƙungiyar ta aika wa gwamnatin jihar wasiƙar sanar da aniyarta ta shiga yajin aikin a ranar 7 ga Oktoba, 2026. Sai dai ya nuna nadama kan yadda yawancin buƙatunsu ba su samu mafita ba, duk da ƙarewar wa’adin da suka bayar.
Balange ya ƙara da cewa matakin ya biyo bayan ƙoƙarin da ƙungiyar ta sha yi na tattaunawa da gwamnati domin cimma matsaya ta lumana kan matsalolin da ke shafar ma’aikatan lafiya a jihar.













