Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning, ta bayyana cewa kasar Sin ta ci gaba da tsayawa kan matsayinta na cewa ya kamata a mutunta tare da kiyaye sakamakon nasarar da aka samu a yakin duniya na kin tafarkin murdiya.
Mao Ning ta bayyana haka ne yayin da ta mai da martani kan adawar da Japan ta bayyana, dangane da ziyarar da tawagar wakilan lardin Heilongjiang na Sin ta kai wasu tsibiran da Japan da Rasha ke takaddama a kansu, a gun taron manema labarai na yau da kullum da aka gudanar yau Laraba.
Dangane da bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin CIIE karo na 9 da za a bude a ranar 5 ga watan Nuwamba, Mao ta bayyana cewa, a wannan shekarar ma bikin zai ci gaba da samar da wuraren baje koli kyauta ga kasashe masu karancin ci gaba.
Bugu da kari, za a inganta sashen baje koli na musamman don kayayyakin da suka fito daga Asiya da Afirka, domin bai wa kasashen Afirka dake da huldar diflomasiyya da Sin damar cin gajiyar manufar soke harajin kwastam.(Safiyah Ma)













