Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun bai wa Ministan Tsaro, Christopher Musa, wa’adin kwanaki bakwai da ya janye zargin da ya yi kan tsohon gwamnan, ko kuma ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da kalamansa.
Zargin ya samo asali ne daga wata hira da ministan ya yi a gidan talabijin na Channels, inda ya danganta El-Rufai da shirya kisan mutane a Kudancin Kaduna. Iyalin El-Rufai sun bayyana zargin a matsayin babban al’amari kuma na bata suna, suna cewa ba tare da gabatar da wata hujja da ke tabbatar da shi ba.
Lauyoyin El-Rufai sun kuma bukaci ministan ya bayar da hakuri a bainar jama’a tare da janye kalaman ta kafar da aka yi amfani da ita wajen yada zargin. Sun kuma bukaci a wallafa janyewar zargin a wasu jaridu na kasa, tare da adana dukkan bayanai da takardun da suka shafi hirar da hujjojin da ministan ya dogara da su.
Baya ga bukatar janye kalaman, lauyoyin sun bukaci Naira biliyan 10 a matsayin diyya, tare da gargadin cewa za su dauki matakin shari’a idan ministan bai biya bukatunsu ba cikin wa’adin kwanaki bakwai ba. Sai dai wasikar ta bayyana cewa wannan kudin bukatar sulhu ne, ba wata diyya da kotu ta yanke ko ta amince da ita ba.
Iyalan tsohon gwamnan sun ce idan ministan yana da hujjojin da ke tabbatar da zargin, ya gabatar da su, amma idan babu su, su na bukatar ya janye kalaman tare da ba da hakuri. Sun kuma yi barazanar daukar dukkan matakan shari’a da suka dace idan wa’adin ya cika ba tare da an warware lamarin ba.














