A yau Talata ne kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Chen Xi, ya amsa tambayoyin manema labarai dangane da takardar bayani kan harkokin tsaro ta 2026 da gwamnatin Japan ta fitar.
Chen Xi, ya ce sabuwar takardar bayanin da Japan ta fitar na cike da karairayi, da zuzuta batun da ya shafi matsalolin tsaro, tare da yayata zargin wai “Sin na zama barazana”.
Jami’in ya kara da cewa, hakan tamkar “Kura ce ke cewa da kare maye”, wato Japan na kokarin zakulo wasu abubuwan fakewa, don cimma muradun sassauta kaidin dake wuyanta ta fuskar soji.
Chen, ya kuma ce Sin na kira ga Japan da ta zurfafa nazari kan abubuwan da ta aikata na danniya a tarihi, ta dakatar da kawar da hankulan al’ummunta, da ma na sauran sassan kasa da kasa daga gaskiya, kana ta dakatar da kara zurfafa tafiya kan turbar kuskure ta farfado da karfin rundunar soji. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














