Sama da kwanaki tamanin da kai hari da yin garkuwa ga fasinjojin jirgin kasa a Kaduna, sama da mutum 50 da suka hada da mata, yara, manya da kananan har yanzu su na hannun ‘yan garkuwa da mutanen cikin mayuwacin hali da kuncin rayuwa.
Bayanai da suke fitowa na nuna da cewa tabbas halin da fasinjojin ke ciki ya munana don kuwa macizai da kunamu suna kai musu farmakin inda zuwa yanzu aka samu rahoton cewa mutum 9 daga cikinsu sun mutu sakamakon wannan saran da macizai da kunamai suke musu.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin mai bai wa Sheikh Ahmad Gumi shawarwari a bangaren yada labarai, Malam Tukur Mamu, wadda ya shiga tsakani aka samu nasarar sako mutum 11 daga hannun masu garkuwan.
A cewarsa, wannan lamarin na faruwa ne sakamakon dajin da masu garkuwan suka ajiye fasinjojin na fuskantar ruwan sama don haka macizai kan fito daga cikin ramuka don sauya wajen zama a irin wannan yanayin ne suka haduwa da mutanen tare da sararsu.
Rahoton ya kuma yi zargin cewa, ana fargabar sama da mutum 9 daga cikin fasinjojin sun mutu a sakamakon wannan mummunar yanayin da suke ciki a yanzu haka.
A cewar Mamu, mafiya yawa daga cikin fasinjojin zai yi matukar wuya su iya cigaba da rayuwa idan aka shafe wasu karin makonni a hannun masu garkuwan lura da yanayin halin lafiyarsu da ya tabarbare ba tare da kuma samun kulawar maganin da suka dace ba a cikin dajin.
Har-ila-yau, ya ce akwai bukatar gwamnati da masu ruwa da tsaki kan lamarin su kara azama domin ganin an cetosu da ransu daga hannun ‘yan garkuwan.
LEADERSHIP HAUSA ta labarto cewa, ‘yan ta’addan sun kai hari ga jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ne a ranar 28 ga watan Maris din 2022 tare da kashe mutum 9 hadi da yin garkuwa da a kalla mutum 63 da suke cikin jirgin ciki hard a manajan gudanarwa na bankin BOA, wanda aka sakeshi bayan zargin ahlinsa sun biya miliyan 100 na diyyarsa.
Mamu, wanda mawallafin jaridar ‘Desert Herald’ ne, ya ce, tuni ya sanar da shugabannin Nijeriya, jami’an tsaro, da masu ruwa da tsaki kan halin da ake ciki domin daukan matakan da suka dace na gaggauta ceto fasinjojin lura da hadin kunci da suke ciki.
“Yanzu ba lokacin batutuwan da suka shafi siyasa ba ne, rayukan mutane na da matukar muhimmanci, raunanan ‘yan Nijeriya na daga cikin wadanda wannan lamarin ya shafa. Yanayin lafiyarsu na kara lalacewa kullum.
Hatta dabbobi da wuya su iya rayuwa a muhallin da ake kuntata musu da tilasta musu, balle mutanen da suka doshi kusan wata uku zuwa yanzu.
“Na yi imanin gwamnati tana sane da ko ta samu bayanai daga mutum 11 da suka kubuta daga cikin wadanda lamarin ya shafa. Abun damuwa ne gare ni idan na ga lamari irin wannan an kasa daukan matakan da suka dace a kai, wanda kuma lallai na bukatar a gaggauta maida hankali sosai wajen yin abun da ya kamata.”
Ya jawo hankalin gwamnati da ta yi amfani da hanyoyi na hikima da diflomasiyya wajen shawo kan matsalolin tare da ceto wadanda suke tsare gami da sauran batutuwan da suka shafi matsalar tsaro fiye da batun zaben 2023.
Sai dai kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ya umarci jami’an tsaro su tabbatar da sun ceto mutanen da ransu tare da sada su da iyalansu.
Mai magana da yawun shugaban kasan, Malam Garba Shehu ya sanar da umarnin na Shugaba Buhari a ranar Talata inda ya kara da cewa gwamnati tana ci gaba da bitar batun wadanda aka sacen kuma ana ci gaba da dukkan kokarin ganin an ceto ragowar da suka rage a hannun ‘yan ta’addan su 51.
Ya kara da cewa, umarnin da Buhari ya bayar baro-baro a fili shi ne a ceto fasinjojin da suka rage da ransu zuwa gida, kuma jami’an tsaro suna sane da aikin da ya rataya a wuyansu kuma sun dukufa wajen aiki da cikawa sakamakon umarnin da shugaban ya bayar.
Iyalan Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su Sun Bayyana Yadda Aka Yi Watsi Da Su
Kazalika, wasu daga cikin iyalan fasinjojin da aka yi garkuwa da su, sun ce, bai dace a dawo jigilar fasinjoji ba har sai an ceto dukkanin fasinjojin da suke hannun masu garkuwa, suna masu cewa akwai kuma bukatar daukan tsauraran matakan kare rayukan da lafiyan fasinjoji kafin dawo da jigilar.
Wadanda suke magana ta bakin kakakinsu, Dakta Abdulfatai Jimoh, iyalan sun zargi hukumar kula da sufurin jiragen kasa a Nijeriya (NRC) da kin mutunta umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na zama tare da su da yin hulda a kai a kai don cimma nasarar ceto wadanda suke tsare.
Jimoh ya kara da cewa, “Mun ji dadi bisa kokarin da gwamnati ta fara yi na tattaunawa da masu garkuwa da ‘yan uwanmu,” ya kuma yi kira ga gwamnatin da ta hanzarta wajen cimma matsaya da masu garkuwan domin makusantan nasu su samu kubuta.
Ya ce, suna kewar ‘yan uwansu tun lokacin da aka sacesu, sai ya gargadi hukumar NRC daga shirinta na dawo da jigilar fasinoji, ya ce muddin ba a samar da wadaccen tsaro ba, babu amfanin dawo da sufurin.
Sai dai kuma Kakakin hukumar NRC, Mahmood Yakub, ya karyata labaran da aka yada na cewa suna shirin dawo da jigilar jirgin kasan a wannan layin dogon da ake batu a kai.
Yakub ya kara da cewa, “Muna yin duk mai yiyuwa domin tabbatar da ceto wadanda suke tsare. Lallai muna kan kokari sosai, mun kuma tattauna da shugaban iyalan wadanda lamarin ya shafa.
“Muna aiki sosai domin ganin dukkanin wadanda aka sace sun fito cikin koshin lafiya. Muna kan kokarin sosai.”