ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Ta Yi Asarar Biliyoyin Naira Saboda Dakatar Da Shigo Da Motoci Ta Iyakokinta

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
Nijeriya

Masu ruwa da tsaki a ɓangaren harkokin jiragen ruwa da kasuwancin kan iyaka sun yi zargin cewa haramcin da gwamnatin tarayya ta sanya kan shigo da motoci ta land borders ya jawo wa Nijeriya asarar biliyoyin Naira na kuɗaɗen shiga a duk shekara, tare da ƙarfafa ayyukan fasa ƙwauri ta hanyoyin da ba a amince da su ba.

Da yake magana kan tasirin wannan manufa, shugaban kuma babban jami’in gudanarwa na kamfanin Only God is Wise Nigeria Limited, wanda ke gudanar da bonded terminal a iyakar Seme Border, Alhaji Adetona Mubashiru, ya buƙaci Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Adewale Adeniyi, da ya tura batun sake duba wannan dokar da aka shafe shekaru tara ana aiwatarwa.

Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta sanar a watan Disambar 2016 cewa ta haramta shigo da sabbin motoci da tsofaffi ta kan iyakokin ƙasa, inda ta umarci cewa duk motocin da za a shigo da su su riƙa zuwa ta tashoshin jiragen ruwa daga ranar 1 ga Janairun 2017.

ADVERTISEMENT

Mubashiru ya bayyana cewa manufar ta gaza cimma burinta na daƙile fasa ƙwauri da inganta sa ido kan motocin da ake shigowa da su. A maimakon haka, ya ce ta karkatar da halalcin kasuwanci zuwa ƙasashe maƙwabta da kuma hanyoyin kan iyaka da ba a amince da su ba.

A cewarsa, dokar ta tilasta masu shigo da kaya amfani da tashoshin jiragen ruwa masu cunkoso, yayin da wasu da dama suka koma amfani da hanyoyin jeji ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ya sa aikin jami’an Kwastam ya fi wahala tare da hana Nijeriya samun manyan kuɗaɗen shiga daga haraji.

LABARAI MASU NASABA

Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano

Fargabar Satar Mutane Ya Sa An Rufe Makarantu A Abuja Da Mararaba

Ya ce: “Maimakon dakatar da shigo da haramtattun kaya, dokar ta mayar da kasuwancin zuwa ɗaruruwan hanyoyin da ba a amince da su ba. Hukumar Kwastam ta fuskanci ƙalubale sosai wajen sa ido kan waɗannan hanyoyi yayin da gwamnati ke ci gaba da rasa kuɗaɗen shiga masu yawa duk shekara.”

Ya ƙara da cewa ƙasashe maƙwabta sun amfana sosai daga wannan manufa, domin masu shigo da kaya da dama sun karkatar da kayansu zuwa tashoshin jiragen ruwa da ke wajen Nijeriya, musamman a Benin Republic, inda ake ci gaba da jigilar motocin da aka nufa zuwa Nijeriya.

Mubashiru ya tunatar da cewa tsohon Kwanturola Janar na Kwastam, Hameed Ali, ya kare manufar a matsayin matakin da zai taimaka wajen yaƙi da takardun bogi da kuma shigo da motoci ba bisa ƙa’ida ba ta kan iyaka.

Sai dai Mubashiru ya dage cewa tun kafin dokar ta fara aiki, akwai yarjejeniya tsakanin Nijeriya da Benin Republic kan sa ido da jigilar motocin transit ta iyakar Seme ƙarƙashin kulawar jami’an Kwastam.

Ya bayyana cewa motocin da ke zuwa daga tashar jirgin ruwa ta Cotonou ana raka su zuwa iyaka sannan a miƙa su ga jami’an Kwastam na Nijeriya domin tantancewa, yana mai cewa matsalolin aiki kamar rashin isasshen filin ajiye motoci an magance su yanzu.

“Yanzu abubuwa sun canza. Iyakar Seme na da wuraren da za su iya ɗaukar motoci sama da 1,000 cikin sauƙi, wanda hakan zai sa tsarin ya zama mai tsari da gaskiya,” in ji shi.

Mubashiru ya kuma ce dokar ta shafi dubban ƴan Nijeriya da rayuwarsu ta dogara da harkar shigo da motoci, ciki har da dillalan kaya, direbobi, bakanikai, masu gyaran motoci da masu fenti da sauran masu sana’o’i a yankunan kan iyaka.

Ya roƙi shugabannin Kwastam na yanzu da su ba gwamnatin tarayya shawarar sake nazarin dokar bisa tsarin sauƙaƙa kasuwanci na duniya da kuma buƙatun masu ruwa da tsaki domin samar da tsarin shigo da kaya mai anfani ga tattalin arziki da gaskiya.

Mubashiru ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa sake buɗe kan iyakoki domin shigo da motoci zai ƙara halalcin kasuwanci, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa kuɗaɗen shiga na gwamnati.

Nijeriya
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
Labaran Kasuwanci

Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano

August 23, 2026
Fargabar Satar Mutane Ya Sa An Rufe Makarantu A Abuja Da Mararaba
Labaran Kasuwanci

Fargabar Satar Mutane Ya Sa An Rufe Makarantu A Abuja Da Mararaba

June 4, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA
Labaran Kasuwanci

Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

May 21, 2026
Next Post
APC Ta Dakatar Da Sanata Kan Zargin Cin Amanarta

APC Ta Dakatar Da Sanata Kan Zargin Cin Amanarta

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.