ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisar Dattawa Ta Tswaita Aiwatar Da Kasafin Kuɗin 2025 Zuwa 30 Ga Watan Satumba

by Sadiq
3 months ago

Majalisar Dattawa ta amince da tsawaita wa’adin aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 da wata uku, inda aka mayar da ranar ƙarshe daga 30 ga watan Yuni zuwa 30 ga watan Satumba, 2026.

An yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis bayan sanatoci sun tattauna kan jinkirin aiwatar da wasu ayyuka da kuma yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka riga aka sakar wa ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati.

Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Sanata Tahir Monguno, ya ce har yanzu ana gudanar da ayyuka da dama kuma suna buƙatar ƙarin lokaci saboda jinkirin saye da samar da kayayyaki, matakan gudanarwa da sauran ƙalubalen aiwatar da ayyuka.

ADVERTISEMENT

Ya bayyana cewa idan ba a tsawaita wa’adin ba, akwai yiwuwar a dakatar da wasu muhimman ayyuka, a yi asarar kuɗaɗen gwamnati da aka riga aka ware, tare da kawo cikas ga shirye-shiryen gwamnati.

Shugaban Kwamitin Kasafi na Majalisar Dattawa, Sanata Solomon Adeola, ya ce tsawaitawar ta shafi ɓangaren ayyukan raya ƙasa ne kawai.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Ya ƙara da cewa har yanzu akwai wasu ayyuka da biyan kuɗaɗe da ba a kammala ba a ƙarƙashin kasafin 2025, wanda ya sa aka ga dacewar ƙara lokaci.

Sanatocin sun amince da ƙudirin gaba ɗaya, sannan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da cewa sabon wa’adin aiwatar da kasafin zai ƙare ne a ranar 30 ga watan Satumba, 2026.

Ya ce matakin zai taimaka wajen tabbatar da kammala ayyukan da ake yi da kuma ci gaba da biyan kuɗaɗen da suka dace ba tare da tangarɗa ba.

A baya, Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta riga ta tsawaita wa’adin aiwatar da kasafin kuɗin 2025 zuwa 30 ga watan Yuni, 2026.

Wannan sabon ƙarin lokaci zai bai wa ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati damar kammala ayyukan da suke yi tare da amfani da kuɗaɗen da aka amince da su yadda ya kamata.

MASU ALAKA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Next Post
Kwararrun Sin Da Na DRC Sun Tattauna Matakan Hadin Gwiwa Na Dakile Cutar Ebola

Kwararrun Sin Da Na DRC Sun Tattauna Matakan Hadin Gwiwa Na Dakile Cutar Ebola

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.