ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Miyetti Allah Ta Yi Barazanar Ƙauracewa APC Kan Ci Gaba da Tsare Boɗejo

by Sulaiman and Zubairu M Lawal
5 days ago
Bodejo

Shugabannin ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore sun yi barazanar cewa za su yi kira ga al’ummar Fulani da su kaurace wa zaɓen Jam’iyyar APC a 2027, matuƙar Gwamnatin Tarayya ba ta saki shugaban ƙungiyar, Alhaji Bello Bodejo ba.

Shugabannin ƙungiyar sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da suka gudanar ranar Laraba a harabar ofishin Bodejo da ke Kasuwar Maliya, Ƙaramar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa, inda suka nuna rashin amincewarsu da ci gaba da tsare shugaban nasu.

A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar na Arewa ta Tsakiya, Alhaji Idris Gidado Bebeji, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi, SAN, da shugabannin APC da hukumomin tsaro da abin ya shafa, da su tabbatar da warware lamarin cikin adalci da bin doka.

ADVERTISEMENT

Ƙungiyar ta ce Bodejo fitaccen jagora ne da ke fafutukar kare muradun Fulani makiyaya, tare da bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

A cewar ƙungiyar, DSS ta kama Bodejo a Jalingo, Jihar Taraba, a ranar da ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar Sanata mai wakiltar Taraba ta Tsakiya. Daga bisani aka miƙa shi ga EFCC, inda ya shafe kusan watanni huɗu a tsare.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Sanarwar ta ce bayan cika wasu sharuddan da suka wajaba domin a sake shi daga hannun EFCC, an sake shi, amma daga bisani DSS ta sake kama shi a ranar 28 ga Agusta, 2026.

Shugabannin ƙungiyar sun ce ci gaba da tsare Bodejo ya jefa dubban zawarawa da marayu cikin ƙuncin rayuwa, musamman yaran da suka ce karatunsu ya tsaya saboda Bodejo ne ke taimaka wajen biyan bukatunsu na yau da kullum.

Da yake jawabi, ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar, Sulaiman Abdullahi, ya ce idan Gwamnatin Tinubu ta ƙi sakin Bodejo, za su yi kira ga Fulani a faɗin Nijeriya da su ƙaurace wa zaɓen APC a 2027.

Ya yi iƙirarin cewa a zaɓen 2023, Bodejo ya taka rawa wajen haɗa kan al’ummar Fulani domin marawa APC baya, yana mai cewa yanzu ƙungiyar za ta iya karkatar da goyon bayan Fulani zuwa wata jam’iyya idan ba a sake shi ba.

Sai dai ƙungiyar ta buƙaci mambobinta da sauran Fulani makiyaya su ci gaba da kasancewa cikin nutsuwa, zaman lafiya da bin doka, yayin da take amfani da hanyoyin kundin tsarin mulki wajen neman a sake shugaban ƙungiyar.

Bodejo
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Bodejo
Zubairu M Lawal
+ posts Bio
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Tsaftar Muhalli: Gwamnatin Nasarawa Ta Rufe Kasuwar Tumatir A Lafia
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Samar Da Abinci Mai Gina Jiki: Gwamna Sule Ya Duba Gonakin Shinkafa A Jangwa
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Tsohon Sufeto Janar Na ‘Yansanda Ya Tallafawa Manoma Da Kayan Aikin Gona Na Miliyoyin Naira A Nasarawa
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Gwamnatin Nasarawa Ta Gargaɗi Masu Tayar Da Fitina Da Sunan Siyasa

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Sarkin Gumel Ya Rasu Yana Da Shekaru 84

Sarkin Gumel Ya Rasu Yana Da Shekaru 84

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.