Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana a yau Talata 18 ga wannan wata cewa, a matsayin kasa da ta sanya hannu kan yarjejeniyar magance kwararar hamada ta MDD, kasar Sin ta sauke nauyin dake wuyanta, na sa kaimi ga hadin gwiwa tare da sassan kasa da kasa wajen magance kwararar hamada. A nan gaba kuma, Sin za ta ci gaba da samar da gudummawa wajen magance kwararar hamada a duk duniya.
An kaddamar da taron sassan da suka sanya hannu kan yarjejeniyar magance kwararar hamada ta MDD karo na 17, a birnin Ulaanbaatar dake kasar Mongolia a jiya Litinin 17 ga wannan wata. Game da wannan batu, Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin na nacewa tunanin tabbatar da ruwa mai tsafta, da tsaunuka masu kima, a matsayin kadarori masu daraja da za a iya kwatanta su da zinariya da azurfa, kana ta zama kasa ta farko da ta cimma burin hana karuwar lalacewar kasa a duniya, da rage fadin kasar hamada, da kiyaye karuwar yawan bishiyoyi da shekaru 40 a jere, ta yadda ta samar da muhimmiyar gudummawa wajen cimma burin dakile karuwar lalacewar kasa nan zuwa shekarar 2030 a duniya.
Lin Jian, ya kuma ce sakatariyar kwamitin yarjejeniyar, ta gabatarwa Sin da lambar yabo ta kasa mafi bayar da gudummawar magance kwararar hamada, da ayyana kasar ta Sin a matsayin misali ga duniya a wannan fanni. (Zainab Zhang)














