ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matakin Kawar Da Harajin Kwastam Da Sin Ta Ayyana Zai Karfafa Cinikayya Da Kasashen Afirka

by Sulaiman and CGTN Hausa
5 months ago
Sin

Mahalarta taron masu ruwa da tsaki dangane da hada-hadar zuba jari na Gauteng, wanda ya gudana a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu a kwanan baya, sun yi hasashen yadda matakin janye dukkanin harajin kwastam kan hajojin kasashen Afirka da ake shigarwa kasuwannin Sin, zai taimaka wajen bunkasa cinikayya da tattalin arzikin kasashen nahiyar.

Da yake tsokaci game da hakan, babban jami’in shirin “Proudly South African”, wani shiri dake rajin ingiza sayayyar hajoji da hidimomi da ake samarwa a cikin Afirka ta kudu, mista Eustace Mashimbye, ya ce matakin na gwamnatin kasar Sin, zai taimaka wajen bunkasa kasuwanci a kasar, da ma raya tattalin arzikin dukkanin kasashen Afirka. Mashimbye ya ce “Manufar Sin ta janye harajin za ta yi matukar amfanar ‘yan kasuwar Afirka ta kudu, kuma hakan dama ce da kasashen nahiyar suka jima suna jira”.

Kazalika, Mashimbye ya ce manufar za ta bude managartan kofofi na shiga kasuwa mafi girma a duniya, tare da samar da damammaki na hakika, wadanda za su haifar da ci gaba, da bunkasa masana’antu, da guraben ayyukan yi a dukkanin sassan Afirka.

ADVERTISEMENT

A nasa bangare kuwa, babban jakada a ofishin jakadancin Sin dake birnin Johannesburg Pan Qingjiang, cewa ya yi ana sa ran manufar za ta yi matukar bunkasa cinikayya, da yaukaka alakar tattalin arziki tsakanin Sin da Afirka. Ya ce a gabar da Sin ke kara azamar aiwatar da manufar yafe dukkanin harajin kwastam ga kasashen Afirka, Sin da Afirka ta kudu na kuma aiwatar da tsare-tsare na kut-da-kut, don tabbatar da nasarar manufar, da cimma cikakkiyar gajiya daga gare ta.

Bugu da kari, jami’in ya ce manufar za ta samar da gagarumin alfanu ga al’ummun Afirka, yayin da su kuma masu sayayya na Sin, za su ci gajiyar karin hajoji masu inganci daga kasashen Afirka. (Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

September 8, 2026

Next Post
Binciken CGTN Ya Nuna Sama Da 80% Na Masu Bayyana Ra’ayoyi Na Zargin Kasar Japan Da Gurgunta Alakarta Da Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Sama Da 80% Na Masu Bayyana Ra’ayoyi Na Zargin Kasar Japan Da Gurgunta Alakarta Da Sin

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci