ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, October 28, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna

by Sani Anwar
4 days ago

Ƙungiyar Yaqin Neman Zaben Shugaban Kasa ta Makinde-Daura (MDPCO), ta bayyana qaddamar da yaqin neman zaven Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shekarar 2027 a Jihar Kaduna a ranar Asabar, wacce ba za ta iya ceto shi daga shan kashi a hannun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APM ba, Injiniya Seyi Makinde.

Manufofin Shugaba Tinubu masu matukar tsanani, wadanda suka jefa miliyoyin ‘yan kasa cikin halin kunci da barazanar rayuwa, sun kasance a matsayin wasu alamun gazawa da suka sa ‘yan Nijeriya suka yi watsi da shi da jam’iyyarsa ta APC.’Yan Nijeriya ba sa tsammanin komai daga wannan kaddamarwar ta Tinubu, face irin yadda aka saba ji na zuba karya, yaudara, alkawuran da ba su da tushe da kuma iqirarin ayyukan da ba su taba faruwa ba, duk wadannan daga shugabannin APC da suka rasa amincewar jama’a da kuma ‘yan siyasa masu damfara wadanda kwadayi da son mulki suka hada su wuri guda.

Kasancewar Shugaba Tinubu ya zabi kaddamar da yakin neman zabensa na 2027 a Kaduna, wacce ita ce cibiyar siyasar Arewacin Nijeriya, muna kalubalantarsa da ya bayyana abin da yankin ya samu daga gwamnatinsa mara kwarewa, wacce ta fi mayar da hankali kan nuna fifiko ga ‘yan’uwa da abokan arziki (nepotism). Shin akwai abin da ya wuce yawaitar zubar da jini, tsananin wahalar rayuwa, qarya alkawura da kuma rushewar amincewar jama’a a gare shi?

ADVERTISEMENT

Ƴan Nijeriya za su tuna cewa, a taron yakin neman zaben jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kaduna a ranar 13 ga Disambar 2022, Tinubu ya yi ikirarin cewa; “Dukkan masu tayar da hankali da masu garkuwa da mutane da masu kisa, wadanda ke barazana ga tsaron Kaduna da Arewacin Nijeriya, ina ba ku tabbacin cewa; za mu kawar da su.” Ya kuma yi alkawarin cewa, za a tabbatar da tsaro da kare kowane yanki na kasar Nijeriya.

Shekaru uku da rabi bayan nan, a karkashin mulkinsa, ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda na ci gaba da kashe mutane da yin garkuwa da su da kuma tilasta wa ‘yan kasa barin muhallansu a yankin Arewa maso Yamma da sauran sassan Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

INEC Ta Fara Gyaran Rajistar Masu Zaɓe Bayan Zargin Amfani Da Hotunan AI

Zan Yi Wa Tinubu Kamfen Idan Ya Magance Matsalar Tsaro – Bafarawa

Tun bayan da Shugaba Tinubu ya hau karagar mulki a shekarar 2023, wadanda aka kashe ba su gaza qasa da 13,000 a yankunan Arewacin kasar ba, yayin da aka sace wasu da dama. A duk wannan lokacin, abin da Shugaba Tinubu yake yi kawai shi ne, bayar da umarni daga fadar shugaban kasa (Villa) da kuma fitar da sanarwar manema labarai marasa tasiri, ba tare da daukar wani mataki na zahiri, don magance matsalar rashin tsaro a yankin da sauran sassan Nijeriya ba.

MDPCO ta ce, babu wani yanki na kasar da ya kamata ya zama rumbun adana zave da za a kai hari, duk bayan shekara hudu, kuma a yi watsi da shi bayan samun nasara. ‘Yan Nijeriya, duk inda suke, sun cancanci fiye da alkawarin kamfen; sun cancanci tsaro, rayuwa mai araha, samun bunkasar gonaki, wutar lantarki mai inganci, ingantaccen ilimi da shugabanci mai inganci da amana. Babu wani yanki na kasar da ya kamata ya zama tushen samun kuri’u ga masu iko da kuma za a yi sakaci da shi.

Takardar sanarwar da Richard Nnanna IhediwaDaraktan Sadarwa Na MDPCO ya sanya wa hannu ta ci gaba cewa, ya kamata Shugaba Tinubu ya fahimci cewa, ya gaza kuma ‘yan Nijeriya sun kuduri aniyar maye gurbinsa da Injiniya Seyi Makinde, wanda Ajandarsa ta ‘RESET NIGERIA’, ta samar da madadi bayyananne; mutane kafin iko, tsaro kafin farfaganda da jin daxin jama’a kafin gata na manyan mutane. Nijeriya na buqatar shugabanci, wanda ke isar da saqo, ba shugabancin da ke yaudara ba.

Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Shirin Sulhu Tsakanin Kwankwaso Da Abba: Ina Aka Dosa?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi

MASU ALAKA

INEC Ta Fara Gyaran Rajistar Masu Zaɓe Bayan Zargin Amfani Da Hotunan AI
Siyasa

INEC Ta Fara Gyaran Rajistar Masu Zaɓe Bayan Zargin Amfani Da Hotunan AI

October 28, 2026
Zan Yi Wa Tinubu Kamfen Idan Ya Magance Matsalar Tsaro – Bafarawa
Siyasa

Zan Yi Wa Tinubu Kamfen Idan Ya Magance Matsalar Tsaro – Bafarawa

October 28, 2026
Ban Taɓa Faɗin Mummunan Abu Kan El-Rufai Ba – Uba Sani
Siyasa

Ban Taɓa Faɗin Mummunan Abu Kan El-Rufai Ba – Uba Sani

October 28, 2026
Next Post
Magoya Bayan ‘Tinubu Must Come’ Da ‘Tinubu Must Go’ Sun Yi Arangama

Magoya Bayan ‘Tinubu Must Come’ Da ‘Tinubu Must Go’ Sun Yi Arangama

LABARAI MASU NASABA

TUC Ta Yi Watsi Da Ƙarin Tallafin Sufuri Na ₦70,000, Ta Nemi A Biya Mafi ƙarancin Albashin ₦300,000

TUC Ta Yi Watsi Da Ƙarin Tallafin Sufuri Na ₦70,000, Ta Nemi A Biya Mafi ƙarancin Albashin ₦300,000

October 28, 2026
INEC Ta Fara Gyaran Rajistar Masu Zaɓe Bayan Zargin Amfani Da Hotunan AI

INEC Ta Fara Gyaran Rajistar Masu Zaɓe Bayan Zargin Amfani Da Hotunan AI

October 28, 2026
Zan Yi Wa Tinubu Kamfen Idan Ya Magance Matsalar Tsaro – Bafarawa

Zan Yi Wa Tinubu Kamfen Idan Ya Magance Matsalar Tsaro – Bafarawa

October 28, 2026
Babban Hafsan Sojojin Nijeriya Ya Goyi Bayan Kera Makamai A Cikin Gida Nijeriya

Babban Hafsan Sojojin Nijeriya Ya Goyi Bayan Kera Makamai A Cikin Gida Nijeriya

October 28, 2026
Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Jawo Hankalin Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe 120

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Jawo Hankalin Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe 120

October 28, 2026
Ban Taɓa Faɗin Mummunan Abu Kan El-Rufai Ba – Uba Sani

Ban Taɓa Faɗin Mummunan Abu Kan El-Rufai Ba – Uba Sani

October 28, 2026
EFCC Ta Sake Buɗe Binciken Zarge-Zargen Cin Hanci Kan Atiku

Shirin Tinubu Na Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 20.5 Ya Tabbatar Da Hasashena – Atiku

October 28, 2026
2027: Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen NDC Ya Buƙaci Atiku Ya Marawa Tafiyar Obi-Kwankwaso Baya

2027: Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen NDC Ya Buƙaci Atiku Ya Marawa Tafiyar Obi-Kwankwaso Baya

October 28, 2026
Mutum Biyar Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Ayarin Motocin Gwamnan Neja A Minna

Mutum Biyar Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Ayarin Motocin Gwamnan Neja A Minna

October 28, 2026
Hada-Hadar Yawon Shakatawa A Cikin Gidan Sin Ta Bunkasa Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana

Hada-Hadar Yawon Shakatawa A Cikin Gidan Sin Ta Bunkasa Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.