ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Wakar Mahakar Tagulla Ta Chambishi Ke Samun Farin Jini

by Sulaiman and CGTN Hausa
4 months ago
Chambishi

Yau ita ce Ranar Afirka, ranar da ke tunawa da samun ’yancin kan al’ummun kasashen Afirka daga mulkin mallaka, wadda kuma ke dauke da burin ’yan Afirka na fita daga talauci da zamanantar da kasashensu. Jama’a, a wannan rana ta musamman, ina so in gabatar muku wata waka da ta yi matukar samun farin jini ta yanar gizo kwanan nan, tare da labarin da ke cikinta. Wakar da ma’aikatan Kamfanin NFCA(Non-Ferrous Company-Africa Mining) da ke Zambiya suka rera ita ce “Wakar Mahakar Tagulla ta Chambishi”. “Down, then up again…” wakar ba kawai ta ba da labarin farfadowar wannan mahakar tagulla mai tsawon tarihi na sama da shekaru 100 ba, har ma ta nuna hadin gwiwa da cin gajiyar juna tsakanin Sin da Afirka.

Turawan Ingila ’yan mulkin mallaka ne suka gano mahakar tagulla ta Chambishi a shekarar 1899, kuma mahakar ta dan bunkasa a hannunsu, amma saboda matsalolin fasaha da gudanarwa, aikin hakar tagulla a wurin ya tsaya cik a shekarun 1980. Daga nan, kamfanonin kasashen yamma suka tafi da ribar da suka ci, suka bar mahakar da ma’aikatanta da rashin aikin yi. A shekarar 1998, kamfanin CNMC(China Nonferrous Metal Mining) ya je wajen mahakar tare da jari, fasaha da kuma zumunta, kuma ya daidaita matsalolin da a baya Turawan suka kasa magancewa tare da farfado da mahakar, har ma ya gina mahakar dijital irinta ta farko a Afirka, inda aka kai ga gudanar da ayyukan hakawa da lodawa da kuma jigila, da injuna da fasahohin kirkirarriyar basira, matakin da ya yi matukar inganta ayyukan ma’aikatan. A lokaci guda, CNMC ya dogara ga mahakar Chambishi wajen fadada masana’antu masu alaka, ciki har da samar da injuna da harhada sinadarai da jigilar kayayyaki da sauransu, inda ya gina yankin masana’antu, baya ga kafa yankin hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci na Sin da Zambiya, wanda ya jawo kusan kamfanoni 100, don kara inganta tsarin manasana’antu a kasar. A cikin shekaru 20 da suka wuce, kamfanin CNMC ya zuba jarin da yawansa ya kai sama da dala biliyan 1.6 ga mahakar, kuma ya biya harajin dala miliyan 578, baya ga samar da guraben ayyukan yi sama da 6,200. Ban da haka, ya kuma inganta ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da ci gaban al’ummar garin Chambishi. Abin lura kuma shi ne, a lokacin da yawancin kamfanonin hakar ma’adinai a Zambiya suka dakatar ko rage aikinsu sakamakon matsalar hada-hadar kudi ta duniya da ta kunno kai a shekarar 2008, CNMC ya cika alkawarinsa na “ba za mu rage aikin hakar tagulla ko ton daya ba, kuma ba za mu kori ma’aikaci ko daya ba, kuma ba za mu rage zuba jari ba”, wanda ya tsaya tsayin daka tare da al’ummar wurin don tinkarar kalubalen da suke fuskanta. Don haka tsohon shugaban kasar Zambiya, marigayi Edgar Lungu, ya bayyana CNMC a matsayin “abin koyi ga masu zuba jari na kasashen waje”.

Mahakar Chambishi wani misali ne na hadin gwiwar Sin da Afirka. Da layin dogo na Mombasa zuwa Nairobi a Kenya, da layin dogo mai kwarin daukar nauyi na farko a hamada da ke kasar Aljeriya, da kuma tashar jiragen ruwa mai zurfi ta Lekki a Najeriya, kasar Sin ta taimaka wajen gina manyan ayyukan more rayuwa masu yawa a fadin Afirka, wadanda suka inganta hadewa da juna a tsakanin sassan nahiyar da ma sauran sassan duniya, baya ga bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasashen. Har ila yau, daga samar da fasahar noman da ake kira Juncao wajen taimaka wa makiyaya a Mauritania kiwon tumaki, zuwa dakin gwaje-gwajen hadin gwiwa na rigakafin cututtuka da kiwon lafiyar jama’a tsakanin Sin da Tanzaniya, zuwa kawar da gaba dayan harajin fito kan kayayyaki daga kasashen Afirka 53 da ke da huldar diflomasiyya da kasar Sin, hadin gwiwar Sin da Afirka a fannoni daban daban, yana kyautata rayuwar al’ummar kasashe daban daban a Afirka.

ADVERTISEMENT

“Steel in the silence, the town stays alive…Chambishi Copper Mine, Rise again, rise again…”,dalilin da ya sa wakar mahakar tagulla ta Chambishi ta ke samun farin jini matuka, ba kawai sabo da sautinsa mai dadin sauraro ba ne, har da yadda ta bayyana burin da al’ummar wurin suke son cimmawa game da samun aikin yi da muhallin zama da kyakkyawar makoma. Wakar ta kuma shaida cewa, ingantaccen hadin gwiwa sai da cin gajiyar juna.

A daidai lokacin da muke murnar Ranar Afirka, muna kara yin imanin cewa hadin gwiwar Sin da Afirka bisa manufar rikon gaskiya, kaunar juna da sahihanci, zai ci gaba da rubuta irin labaran yadda Sin da kasashen Afirka ke cin moriyar juna, tare da matse kaimin farfadowar nahiyar Afirka, da kuma taimakawa Sin da Afirka su cimma burin zamanantar da kansu.

LABARAI MASU NASABA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Chambishi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Hisbah Ta Cika Hannu Da Fitaccen Ɗan TikTok A Kano Kan Bidiyoyin Rashin Da’a
  • Sulaiman
    Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC
  • Sulaiman
    ’Yansanda Sun Ceto Mutane, Sun Daƙile Harin ’Yan Bindiga A Katsina
  • Sulaiman
    Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku
Chambishi
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Manufar Sin Kan Raba Fasahar AI Ga Saura: Hakika Mai Bayarwa Ba Ya Rasawa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Na’urar Kiwon Lafiya Ta Sadarwa Tsakanin Kwakwalwa Da Na’ura Mai Amfani Da AI
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Ya Taya Jami’ar Jilin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

MASU ALAKA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka
Ra'ayi Riga

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

September 14, 2026
Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Next Post
Sin Na Jinjinawa Kwazon Pakistan Na Shiga Tsakani Domin Maido Da Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya

Sin Na Jinjinawa Kwazon Pakistan Na Shiga Tsakani Domin Maido Da Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya

LABARAI MASU NASABA

An Ci TikTok Tarar Fam Miliyan £12.7 Kan Karya Dokar Kananan Yara A Burtaniya

Hisbah Ta Cika Hannu Da Fitaccen Ɗan TikTok A Kano Kan Bidiyoyin Rashin Da’a

September 17, 2026
Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC

Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC

September 17, 2026
Kawayen amarya

’Yansanda Sun Ceto Mutane, Sun Daƙile Harin ’Yan Bindiga A Katsina

September 17, 2026
Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku

Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku

September 17, 2026
Nazarin CGTN: Dole Ne Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Samar Da Tsaro Mai Dorewa

Nazarin CGTN: Dole Ne Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Samar Da Tsaro Mai Dorewa

September 16, 2026
Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York

Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York

September 16, 2026
Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Taron Dandalin Xiangshan Da Ake Gudanarwa Kan Sha’anin Tsaro A Beijing

Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Taron Dandalin Xiangshan Da Ake Gudanarwa Kan Sha’anin Tsaro A Beijing

September 16, 2026
Wani Mai Taɓin Ƙwaƙwalwa Ya Kashe Soja A Legas

Sojoji Sun Hallaka Wani Jagoran ’Yan Ta’adda A Katsina

September 16, 2026
Lee Ka Chiu: Shirin Shekaru 5 Na Farko Na Raya Yankin Musamman Na Hong Kong Ya Dace Da Muradun Kasar Sin

Lee Ka Chiu: Shirin Shekaru 5 Na Farko Na Raya Yankin Musamman Na Hong Kong Ya Dace Da Muradun Kasar Sin

September 16, 2026
Gwamnatinmu Za Ta Kawar Da Talauci Da Zarar An Zabe Mu – Shettima

Gwamnonin Arewa 6 Kacal Ne Suka Goyi Bayan Tinubu A 2023 – Shettima

September 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.