Akwai abubuwa da dama da ke jawo zafin tafin ƙafa, mutum ya ji kamar ana ƙona shi? Don haka, dazarar mutum ya fuskanci irin wannan yanayi ko alama, kada ya sake ya yi da shi.Ga wasu daga cikin abubuwan da kan iya jawo wannan zafin tafi na ƙafa kamar haka:
1- Lalacewar jijiyoyi; Lalacewar jijiyoyi na ɗaya daga cikin waɗannan alamomi, musamman ga masu ciwon sikari (Diabetes). 2- Akwai ƙarancin bitamin B (B12, B1, ko B6). 3- Tsayuwa ko tafiya na dogon lokaci, shi ma na kawo wannan zafi na tafi. 4- Sanya takalma masu matse ƙafa ko marasa dacewa, kamar sau ciki da sauran makamantansu. 5- Ƙurajen ƙafa (fungal infection/athlete’s foot), su ma na taimakawa wajen haifar da wannan zafi na tafin ƙafa. 6- Matsalolin zagayawar jinni: Idan jini ba ya samun damar zagawa yadda ya kamata a jikin mutum, wannan ma na iya haddasa zafin tafin ƙafa. 7- Akwai kuma illar wasu magunguna: Ma’ana, sakamakon shan wasu magunguna, daban da daban, hakan ma na taimakawa wajen haifar da wannan zafi na tafin ƙafa.
Me Ya Kama A Yi Idan An Samu Kai A Irin Wannan Yanayi?
– Idan aka yi tsayuwa ko tafiya ta dogon lokaci, sai a samu a huta sosai. – Ka tabbata ka sanya takalma masu dacewa da ƙafarka. – Ka ci abinci wanda ke da wadatar vitamin B. – Idan kana da ciwon siga, ka tabbatar kana sarrafa sigan yadda ya kamata.
A Yi Ƙoƙarin Garzayawa Asibiti Idan:
– Zafin yana ƙaruwa ko bai daina ba.- Kana jin suma, ɗaci ko rashin jin tafin ƙafa. – Ƙafar ta kumbura ko ta yi rauni ko kuma ta canza launi. – Kana da ciwon siga, kuma ka fara jin wannan zafin.
Har ila yau, ya kamata a tuna cewa; zafin tafin ƙafa, alama ce, ba cuta ba. Don haka, yana da muhimmanci a gano ainihin abin da ke haddasa shi, domin a ba da maganin da ya dace.














