A ranar 27 ga watan Yulin da ya gabata, aka haska fim din dake dauke da labarin gaskiya, ko “documentary”, dangane da tsibirin Diaoyu Dao. Fim din mai suna “Diaoyu Dao: Small Island, Big Stakes”, kafar CGTN ta Sin ce ta tsara shi, tare da fara nuna shi a sassan kasa da kasa.
Fim din ya mayar da hankali ga batun rashin jituwa tsakanin Sin da Japan game da ikon mulkin tsibirin Diaoyu Dao, da sauran tsibirai dake kewaye da shi. An dauki fim din a sassan kasar Sin, da Japan, da Amurka, da Birtaniya, ya kuma tattaro ra’ayoyin kwararru Sinawa sama da 30, da kwararrun kasa da kasa a fannin siyasa, tarihi da shari’a.Kazalika, Fim din ya zanta da kusoshin sassa daban daban da suka ganewa idanunsu abubuwan da suka auku a tarihi.
Ta amfani da dalilan tarihi na hakika, da ka’idojin shari’a don tantance tushen batun, fim din ya gabatar da bayanai dalla-dalla, da hotuna na 3D, da hotunan sassa daban daban na hakika na tarihin tsibirin Diaoyu Dao.
A zamanin yau, lokacin da kasar Japan ke aiwatar da manufofin sabunta karfin soji, kuma masu tsattsauran ra’ayi na kasar ke kara fadada karfinsu, waiwayen tarihi, da tantance gaskiyar lamura, za su taka rawar gani na hakika. Baya ga sa-in-sa, gaskiya na da muryarta ta kashin kai. (Saminu Alhassan)













