Ministan tsaron kasar Sin Dong Jun, ya ce rundunar ‘yantar da al’ummar kasar Sin ko PLA, za ta kara azamar inganta zamanantar da tsarin tsaron kasa, da rundunar sojojin kasa, da gaggauta bunkasa shirin tunkarar abokan gaba.
Dong, ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa, yayin babban taron ma’aikatarsa da ya gudana a yau Asabar daya ga watan Agusta, a babban dakin taruwar jama’a, domin bikin cika shekaru 99 da kafuwar rundunar PLA.
A cikin jawabin nasa, ministan tsaron ya jaddada aniyar kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana, yana mai cewa rundunar sojojin kasar Sin za ta kasance cikin shirin sauke nauyin da ke wuyanta, na tabbatar da dinkewar sassan kasar wuri guda, da dakile duk wani yunkuri ‘yan aware masu rajin neman “’Yancin kan Taiwan”, ko tsoma hannun dakarun ketare cikin harkokin gidan kasar Sin.
Dong Jun, ya ce rundunar sojojin kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkanin bangarorin shari’a, wajen nuna adawa da ayyukan da ka iya gurgunta yanayin zaman lafiya, da daidaiton shiyyarsu, da shawo kan tarin kalubalen tsaron duniya, da aiwatar da matakai na hakika, da sauke nauyi irin na rundunar soji ta babbar kasa a duniya. (Saminu Alhassan)














