Sin da Afirka sun ƙaddamar da shirye-shiryen haɗin gwiwa a sashen likitanci jiya Litinin, da nufin sabunta ayyukan kiwon lafiyar al’ummar nahiyar, a matsayin wani ɓangare na zurfafa tsarin haɗin gwiwa a aikace game da kiwon lafiyar jama’a na Sin da Afirka.
Taron wanda aka shirya bisa haɗin gwiwa tsakanin Asibitin Ɗiangya na Jami’ar Tsakiyar Kudanci ta ƙasar Sin, da Babban Asibitin Hanyar Siliki na Addis Ababa, da kuma Asibitin Kawancen Sin da Afirka, ya kasance na ƙaddamar da shirin haɗin gwiwa na Sin da Afirka a ɓangaren likitancin warkar da marasa lafiya ta hanya mai sauƙi, tare da ƙaddamar da cibiyar horaswa kan tiyatar mutum-mutumin na’ura ta Sin da Afirka, da kuma cibiyar horaswa kan fasahar duba marasa lafiya ta hanyar amfani da kananan kayan aiki masu kamara ta Sin da Afirka.
Da yake jawabi ga mahalarta taron, shugaban kasar Habasha, Taye Atske Selassie ya jaddada muhimmancin shigar da fasahar zamani da kuma samar da ƙwararrun ma’aikatan kiwon lafiya a ɓangaren kula da lafiyar al’umma.
Musamman ma, shugaban ya yaba wa masu horarwa da likitoci na ƙasar Sin saboda jajircewarsu wajen bayar da horo da ilimi da kuma ƙwarewa, inda ya bayyana hakan a “matsayin mataki mai matuƙar muhimmanci wajen inganta ayyukan kiwon lafiyarmu, da samar wa da kawunanmu sararin amfani da sabuwar fasaha, da kuma zama a sahun gaba ta fuskoki da dama.”
Ana sa ran sabbin shirye-shiryen da aka ƙaddamar za su zurfafa haɗin gwiwa na dogon lokaci tsakanin cibiyoyin kiwon lafiya na Sin da Afirka ta hanyar haɓaka samar da ƙwararru na musamman ga Afirka ta fuskar ba su jagoranci cikin tsari, da horaswa bisa amfani da na’urar kwaikwayon abubuwa tamkar na gaske, da koyarwa da duba marasa lafiya a aikace a fannin dabarun tiyata na ƙananan kayan aiki masu kamara da na mutum-mutumin na’ura.
A yayin taron dai, kimanin masu samun horo 40 daga ƙasashen Sudan, Tanzania, Uganda, Ghana, Libya, da Habasha sun shiga cikin shirin horaswa na farko kan fasahar amfani da ƙananan kayan aiki masu kamara wanda ƙwararru na ƙasar Sin suka gudanar.














