Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci kasar Kyrgyzstan don halartar taron koli na kungiyar hadin kan Shanghai ko SCO na shekarar 2026, ya kuma gudanar da ziyarar aiki a Kyrgyzstan da Masar, tsakanin ranakun 30 ga watan Agusta zuwa 3 ga watan Satumban nan, bisa gayyatar da aka yi masa. Albarkacin kammala ziyarar, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gabatar da karin bayani kan wannan ziyara ga ‘yan jarida da suka raka shi.
Wang Yi, ya bayyana cewa, shugaba Xi ya gudanar da wannan ziyara ne bisa tushen hadin kai, ya kuma mayar da hankali kan kafa kyakkyawar makomar al’umma ta bai daya, da bayar da shawarwari na yin adalci da gaskiya. Ziyarar tana da muhimmanci da ma’ana mai zurfi, a fannonin cimma matsaya daya tsakanin mabambantan bangarori kan hadin gwiwa, da kuma yin kwaskwarima da kyautata tsarin shugabancin duniya.
Kafafen yada labarai na kasar Sin da na kasashen waje, sun ba da muhimmanci sosai ga wannan ziyara, suna masu ganin cewa, ziyarar ta biya bukatun al’ummun duniya na neman zaman lafiya, da kwanciyar hankali da ci gaba, duba da yadda ake fuskantar rarrabuwar kawuna na siyasar duniy, kuma an yi illa ga tsari da odar kasa da kasa, ziyarar ta samar da dabarar Sin da hikimarta ga duniya mai fuskantar rikice-rikice da sauye-sauye. (Amina Xu)














