Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa an samu ƙaruwar mutane 355,000 da ke amfana da Inshorar lafiya wanda yawan su ya kai 355,000 a shekarar 2023 inda adadin ya kai 583,460 a wannan shekarar kimani kaso 64 a cikin shekaru uku
Raɗɗa ya bayyana haka a ranar juma’a a lokacin da ke ƙaddamar da wasu ƙarin mutane 184,105 cikin shirin Inshorar lafiya da suka haɗa mazaɓo 361 na faɗin jihar Katsina
A cewar sa, sakamakon yana tafiya da kudirin gwamnatin sa na zuba jari da faɗaɗa ingancin kiwon lafiya tare da tabbatar da cewa talaka ya amfana.
“Ayau (juma’a) ba wai muna ƙaddamar da shirin ba ne. Muna ƙara ɗaukar wani matsayi ne da zai kai ga samar da ingantaccen kiwon lafiya da al’umma wanda yake damar su ce ba wai alfarma ba, a matsayin na ƴa ƴan jihar Katsina” inji Raɗɗa
Kazalika ya ƙara da cewa jihar Katsina ta zama ɗaya daga jihohin Nijeriya da suke ɗaukar nauyi na aikin kiwon lafiya na Inshora wanda ya samu lambar yabo a shekarun 2024 da 2025
Haka kuma gwamnan ya bayyana cewa jihohi bakwai sun ziyarci Katsina domin yin koyi da shirin Inshorar lafiya da yadda ake tafiyar da ita a zamanance
Malam Dikko Raɗɗa ya yi bayanin cewa gwamnatin sa ta sake farfarɗo da cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin jihar Katsina tare da kafa kayayyakin zamani da suka da katafaren cibiyar ɗaukar hoto da kuma cibiyar duba masu lalurar kansa da gwaje-gwaje tare da ɗaukaka darajar asibitoci da dama.
Sannan gwamna Raɗɗa ya ce kaso 98 na ma’aikatan jiha da ƙananan hukumomi suna cikin wannan shiri na Inshorar lafiya da kuma waɗanda suka ajiye aiki, da mambobin hukumar Hizba da masu muƙata ta musamman kyauta daga gwamnatin jihar Katsina.
Ya kuma yi bayanin cewa shiga wannan shiri na Inshorar lafiya ƙarƙashin gwamnatin jihar Katsina ya zama wajibi ga dukkanin ma’aikatan gwamnati.
Tunda farko da yake jawabi kwamishinan lafiya na jihar Katsina Hon. Musa Adamu Funtua ya ce gwamnatin Dikko Raɗɗa ta farfaɗo da ƙananan asibitoci 200 tare da ɗaukar ma’aikatan lafiya 1,000 tare da faɗaɗa kuɗaɗen magunguna zuwa kaso 400 da kuma ƙara adadin masu amfana da kiwon lafiya kyauta zuwa 207














