Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna Ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa nasarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, a zaɓen 2027 za ta zama silar kawo ƙarshen tsarin karɓa-karɓar mulki a Nijeriya.
Shehu Sani ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake jawabi a shirin “Politics Today” na gidan talabijin na Channels TV, inda ya jaddada matsayarsa ta cewa ya kamata a bar yankin Kudancin ƙasar ya kammala wa’adin mulki na shekaru takwas kafin mulki ya sake komawa yankin Arewa.
A cewar tsohon ɗan majalisar, duk da cewa tsarin mulki bai hana Atiku takara ba, ya kamata a yi la’akari da adalci da haɗin kan ƙasa, kamar yadda Arewa ta yi shekaru takwas a ƙarƙashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2023 ba tare da yankin Kudu ya nuna adawa mai tsanani ba.
Sani ya ba da shawarar cewa ya kamata dukkan manyan jam’iyyun siyasa su tsayar da ƴan takara daga yankin Kudu domin su fafata a 2027, inda ya bayyana cewa bayan kammala wannan wa’adi a shekarar 2031, Arewa za ta samu cikakkiyar damar karɓar shugabancin ƙasa ba tare da wata fargaba ko tirjiya ba.
A ƙarshe, ya gargaɗi cewa idan har Atiku ya lashe zaɓen, hakan zai haifar da ɓacin rai da nuna ƙiyayya daga al’ummar Kudancin Nijeriya, yana mai jaddada cewa babu wanda zai so ya jagoranci ƙasar da ke fama da rarrabuwar kai da rikice-rikicen siyasa.














