ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nauru: Ƙasar Da Ba A Wasan Ƙwallon Ƙafa A Duniya

by Abba Ibrahim Wada
1 month ago
Nauru

Yayin da ƙwallon ƙafa ta kasance ɗaya daga cikin wasannin mafiya shahara a duniya, har yanzu akwai wata ƙasa da ba a damu da wasan ba. Ƙasar Nauru, wadda wani tsibiri ne da ke tekun Fasifik, wasan ƙwallon ƙafa bai samu karɓuwa ba.

Amma lamarin ya fara sauyawa bayan da Sifaniya, mai maƙwabtaka da tsibirin ta lashe Gasar Kofin Duniya na shekarar 2026. Nauru ba ta taɓa buga wani wasa na hukumar ƙasa da ƙasa da wata ƙasa ba, sannan ƙasar na da filin wasa guda ɗaya kacal, wanda filayenta ya kasance mai taurin yumɓu maimakon ciyawa.

Duk da cewa mutanen ƙasar na matuƙar sha’awar kallon manyan wasannin gasar Firimiya ta Ingila, kuma yara kan sanya rigunan taurarin ƙwallon ƙafa irin su Lionel Messi da Cristiano Ronaldo, duk wani yunƙuri na taka ƙwallon ƙafa da muhimmanci a Nauru sau da yawa kan fuskanci tirjiya.

ADVERTISEMENT

Nauru ta yi ta yunƙurin samar da tawagar kwallon ƙafa a baya, har yanzu wasan bai samu karɓuwa a ba a ƙasar.

Wani yunƙuri na kusa da suka yi shi ne wasan da aka yi da Nauru da tsuburin Solomon da ƴan ƙasar waje ne ke zaune a wajen a 1994 da kuma tawagar ƴan gudun hijira 2014.

LABARAI MASU NASABA

Tsoffin Shugabannin Hukumar NFF Sun Buƙaci A Naɗa Kwamiti Domin Warware Matsalolin Hukumar

NFF Ta Dakatar Da Alkalin Wasa Sakamakon Kwallon Da Ya Hana A Wasan Doma United Da Enyimba

Mummunan tarihin Nauru na baya ya yi bayanin halin da ya sa ƙasar ta kasa samun hanyar fara wasan da ya fi kowanne ɗaukaka a duniya, ta gaza samun ƴan wasa da kuma magoya baya.

Nauru na kusa da tekun Pacific, kimanin kilomita 2,500 daga arewa maso gabashin Australia. Tarihin tarin duniyar da yankin ke da shi ya samo asali ne saboda tarin sinadarin samar da takin zamani, wanda ya taru saboda yawan kashin da tsuntsaye suke yi a yankin.

Yankin Nauru wanda a baya yake mallakin Australia kafin samun samun ƴancin kai a 1968, yana cike da sinadarin Phosphate da ake takin zamani da shi a ƙarshen shekarun ƙarni na 20. Lokacin da sinadarin ya ƙare, sai yankin ya zama tamkar kufai da yake narkar da abubuwa. A baya an san ƙasar da iƙirarin “Tsuburin farin ciki” amma a yau wani ɓangare mai yawa a tsakiyar ƙasar ba zai zaunu ba a wurin mutane kuma ba za a iya noma a wurin ba.

Dalilin haka ya sa mafi yawan al’ummar ƙasar da ba su fi 12,000 suka mayar da hankali wajen zama a bakin teku. Inda za a iya mora a ƙasar ba shi da yawa, saboda wurin ba zai fi girman murabba’i 21 ba, kuma ƙasar kullum raguwa take, saboda matsala sauyin yanayi da yadda gaɓar ruwa ke ƙara faɗaɗa tana cinye ƙasar.

Lalacewar ƙasar noman Nauru ya tilasta mata shigo da kusan kashi 90 na abincin da ake ci, kuma mafi yawan abincin da ake shiga da shi abincin gwangwani ne da kawai sai dai a ci. Wannan ya sa kashi 69 na mutanen ƙasar suke da ƙiba, yayin da kashi 40 cikin 100 ke da ciwon siga mataki na biyu.

Ɗaya daga cikin hanyoyin da Nauru ke samun kuɗin shiga a yau shi ne wata cibiya da Australia ke amfani da ita wajen tsare ƴan cirani, wadda ƙasar ke kula da iya na tsawon shekaru.

Rayuwar yau da gobe a yankin tana da wuya, yayin da shi kuma wasanni na hutu ne da nishaɗi da motsa jiki. Babban wasan da ya fi zama ruwan dare a Australia shi ne Rules Football, wanda kusan kashi 30 na mutanen ƙasar ke yi. Wasannin tsalle-tsalle da na ɗaga ƙarfe da gina jiki na daga cikin abubuwan da suka shahara a wajen motsa jiki.

A 2028 Nauru na son ƙarɓar wasannin Micronesia, wani tarin wasanni da ya haɗa da na ƙwallon ƙafa. Wannan wata alama ce da ke nuna Nauru na son tsoma kanta cikin harkokin wasanni a duniya.

A baya yunƙurin da aka yi na kawo ƙwallon ƙafa Nauru ya samu koma baya ne dalilin wasa ɗaya tal da aka ba da. An sake wani irinsa shekara biyu baya, lokacin da wani tsohon dan wasan Premier Daɓe Kitson ya jagoranci tawagar Nauru mai mutane 18 suka yi atisaye na makonni biyu.

An tsara wasa ne da za su yi na sada zumunta da ƊLFC, domin bunƙasa rayuwar mazauna yankin da kuma tabbatar da lafiyarsu, sai dai wasan bai yiwu ba saboda dalilin kuɗi, dan haka wasan da aka so a yi na farko da Nauru haka aka ɗaga shi.

Amma yanzu yadda ake so a ɗauki ƙwallo a yankin ya sauya, hukumar ƙwallon ƙafa ta yankin ta ce za ta ɗauki shirin ya zama na dogon lokaci maimakon yin sa cikin gaggawa.

Nauru
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    APC Ta Nemi A Gudanar Da Bincike Kan Farmakin Da A Kai Ofisoshinta A Kaduna
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?

MASU ALAKA

Tsoffin Shugabannin Hukumar NFF Sun Buƙaci A Naɗa Kwamiti Domin Warware Matsalolin Hukumar
Wasanni

Tsoffin Shugabannin Hukumar NFF Sun Buƙaci A Naɗa Kwamiti Domin Warware Matsalolin Hukumar

September 15, 2026
NFF Ta Dakatar Da Alkalin Wasa Sakamakon Kwallon Da Ya Hana A Wasan Doma United Da Enyimba
Wasanni

NFF Ta Dakatar Da Alkalin Wasa Sakamakon Kwallon Da Ya Hana A Wasan Doma United Da Enyimba

September 15, 2026
Manchester Derby: City Ta Nunawa United Kwanji A Old Trafford
Wasanni

Manchester Derby: City Ta Nunawa United Kwanji A Old Trafford

September 13, 2026
Next Post
Ko Kin San…Muhimmancin Cin Kayan Lambu A Kullum?

Ko Kin San…Muhimmancin Cin Kayan Lambu A Kullum?

LABARAI MASU NASABA

Nazarin CGTN: Dole Ne Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Samar Da Tsaro Mai Dorewa

Nazarin CGTN: Dole Ne Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Samar Da Tsaro Mai Dorewa

September 16, 2026
Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York

Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York

September 16, 2026
Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Taron Dandalin Xiangshan Da Ake Gudanarwa Kan Sha’anin Tsaro A Beijing

Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Taron Dandalin Xiangshan Da Ake Gudanarwa Kan Sha’anin Tsaro A Beijing

September 16, 2026
Wani Mai Taɓin Ƙwaƙwalwa Ya Kashe Soja A Legas

Sojoji Sun Hallaka Wani Jagoran ’Yan Ta’adda A Katsina

September 16, 2026
Lee Ka Chiu: Shirin Shekaru 5 Na Farko Na Raya Yankin Musamman Na Hong Kong Ya Dace Da Muradun Kasar Sin

Lee Ka Chiu: Shirin Shekaru 5 Na Farko Na Raya Yankin Musamman Na Hong Kong Ya Dace Da Muradun Kasar Sin

September 16, 2026
Gwamnatinmu Za Ta Kawar Da Talauci Da Zarar An Zabe Mu – Shettima

Gwamnonin Arewa 6 Kacal Ne Suka Goyi Bayan Tinubu A 2023 – Shettima

September 16, 2026
Hanyar Ruwa Ta pinglu Ta Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN

Hanyar Ruwa Ta pinglu Ta Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN

September 16, 2026
peter

Peter Obi Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Sayi Hannun Jarin Matatar Mai Ta Dangote

September 16, 2026
Manufar Sin Kan Raba Fasahar AI Ga Saura: Hakika Mai Bayarwa Ba Ya Rasawa

Manufar Sin Kan Raba Fasahar AI Ga Saura: Hakika Mai Bayarwa Ba Ya Rasawa

September 16, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Mutane 240 Bisa Zargin Laifuka Daban-Daban A Yobe

September 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.