Nijeriya da Amurka sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsarin hadin gwiwa da nufin zurfafa hulɗa da jawo jarin Amurka zuwa fannin hakar ma’adinai a Nijeriya, musamman ma’adinai masu muhimmanci da sarrafa su a cikin gida.
Ministan Ma’adinan Ƙasa, Dele Alake, da Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Christopher Landau, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a New York ranar Laraba.
Yarjejeniyar za ta samar da damar gudanar da harkokin kasuwanci da zuba jari tsakanin kamfanonin kasashen biyu, musamman a fannin bincike da sarrafa ma’adinai, samar da kayayyakin more rayuwa da bunkasa ƙwarewar fasaha.
Mai ba ministan shawara kan harkokin yada labarai, Kehinde Bamigbetan, ya ce yarjejeniyar za ta kara hadin gwiwa wajen tattara bayanan kasa, binciken ma’adinai da kara darajar albarkatun da ake samu a Nijeriya.
A cewar Alake, yarjejeniyar na da muhimmiyar rawar takawa wajen tsara makomar masana’antar hakar ma’adinai ta Nijeriya, musamman ganin cewa kasar na da albarkatun ma’adinai da aka kiyasta darajarsu ta kai dala tiriliyan 700.













