Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen yanayi daban-daban na tsawon kwanaki uku, ciki har da rana, hadari, tsawa da ruwan sama a sassan kasar daga ranar Litinin zuwa Laraba.
A cikin hasashen yanayin na kwanaki uku da ta fitar a Abuja ranar Lahadi, NiMet ta ce za a samu yanayin rana tare da kasancewar gajimare lokaci-lokaci, baya ga tsawa da ruwan sama mai matsakaicin karfi a wasu jihohin Arewa, ciki har da Taraba, Kaduna, Adamawa, Kano da Borno.
Hukumar ta kuma yi hasashen cewa yankin Arewa ta Tsakiya, ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT), Neja, Filato, Nasarawa da Benuwe, zai fuskanci tsawa da ruwan sama mai matsakaicin karfi da safe da kuma rana a tsawon wannan lokaci.
A jihohin Kudancin Nijeriya kuwa, ciki har da Lagos, Ondo, Ogun, Ribas, Bayelsa, Akwa Ibom da Kuros Ribas, NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai matsakaicin karfi a sassa da dama da safe, wanda zai iya ci gaba zuwa rana da yamma.
Hukumar ta shawarci mazauna yankunan da abin ya shafa da kuma masu ababen hawa da su dauki matakan kariya daga ambaliyar ruwa ta kwatsam, iska mai karfi da kuma zamewar ababen hawa a kan hanyoyi a yayin ruwan sama.














