ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ramuwar Gayya: ‘Yan Bindiga Sun Ƙona Fadar Hakimin Yankuzo Bayan Harin Sojoji A Zamfara

by Sulaiman
5 months ago
Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun kai harin ramuwar gayya a ƙauyen Yankuzo da ke ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, inda suka ƙone fadar Hakimin yankin, Alhaji Babangida Hamza, tare da sace kayayyaki bayan wani artabu da suka yi da sojoji na tsawon sa’o’i uku da aka kai maɓoyarsu a yankin.

Rahotanni sun ce maharan, ƙarƙashin jagorancin wani da ake kira Mai Rasha, sun mamaye ƙauyen a ranar Talata, suna harbe-harbe ba kakkautawa kafin su banka wa fadar Hakimin wuta.

“Sun shigo suna harbi kai tsaye suka nufi fadata suka ƙona ta,” in ji Hamza, wanda ya bayyana cewa yana garin Tsafe lokacin da harin ya faru.

ADVERTISEMENT

Ya ƙara da cewa, an samu nasarar kwashe iyalansa zuwa wuri mai tsaro, amma har zuwa yammacin ranar Laraba ba a tantance yawan waɗanda suka mutu ko suka jikkata ba.

Mazauna yankin sun ce maharan sun shafe sa’o’i da dama a ƙauyen — har zuwa misalin ƙarfe 3:30 na rana — suna kwasar kayan abinci da sauran kayayyaki masu daraja daga shaguna daban-daban a wani shirinsu na wawashe dukiya.

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

Hakimin yankin ya bayyana cewa harin ramuwar gayya ne sakamakon samamen sojoji da suka kai sansanonin ‘yan ta’adda kusa da yankin a daren ranar.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
  • Sulaiman
    Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari
  • Sulaiman
    Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya
  • Sulaiman
    Ɗabi’un Annabi (SAW) Kan Abubuwa Na Al’adar Rayuwa

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari
Labarai

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Zamfara
Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Next Post
Yerima Shettima Ya Sha Alwashin Kawo Ci gaba Ga Kaduna Ta Tsakiya

Yerima Shettima Ya Sha Alwashin Kawo Ci gaba Ga Kaduna Ta Tsakiya

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026
Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

September 11, 2026
SAW

Ɗabi’un Annabi (SAW) Kan Abubuwa Na Al’adar Rayuwa

September 11, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

September 11, 2026
Zamfara

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Zamfara

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.