Yayin da ake shirin gudanar da babban zaben 2027, Kwamandan Runduna ta 81 ta Sojin Nijeriya, Manjo Janar Adebayo Babalola, ya umurci jami’ai da sojojin da za a tura aikin tabbatar da tsaro yayin zaɓe da su kiyaye kundin tsarin mulki, mutunta hakkokin dan Adam da kuma kasancewa masu tsaka-tsaki a harkokin siyasa.
Babalola ya bayar da wannan umarni ne a wani taron wayar da kan jami’an tsaro da rundunar ta shirya ranar Laraba, 2 ga Satumba, 2026, a dakin taro na ‘Nigerian Army School of Finance and Administration (NASFA)’, Arakan Barracks, Apapa, Jihar Legas.
Taron ya mayar da hankali ne kan bin doka, nauyin da kundin tsarin mulki ya dora wa sojoji da kuma rawar da rundunar soji ke takawa wajen tabbatar da tsaro yayin zaɓe.
An shirya taron ne domin tabbatar da cewa jami’an sojin da za a tura ayyukan zaɓe sun gudanar da aikinsu cikin kwarewa, sanin hakkokinsu da kuma bin ka’ida kafin zaɓe, lokacin zaɓen da kuma bayan kammala zaɓen.
Kwamandan ya ce gudanar da taron na nuna kudurin Runduna ta 81 na ci gaba da bunkasa kwarewar jami’anta da kuma sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata cikin gaskiya da sanin ya kamata.
Babalola ya gargadi mahalarta taron cewa rashin sanin doka ba zai zama hujjar kare duk wani jami’in da ya aikata ba daidai ba.
Ya kuma bukaci jami’an da su mai da hankali sosai kan karatun da ake gabatar musu, tare da neman karin bayani kan duk wasu batutuwan shari’a ko na aiki da za su iya tasowa yayin gudanar da ayyukan tsaron cikin gida da suka shafi zaɓe.














