Rundunar Sojin Ruwa ta Nijeriya, a Onitsha, ta mika wa Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) buhunan 19 da ake zargin tabar wiwi ce aciki.
An gudanar da mika kayan ne a ofishin NDLEA na Onitsha ranar Talata, bayan jami’an tsaron sun kwato su a garin Atani da ke Karamar Hukumar Ogbaru ta Jihar Anambra.
A cewar takardar mika kayan da wakilin jaridar Punch ya samu ranar Laraba, Kwamandan Rundunar Sojin a Onitsha, Kabir Yusuf, ya bayyana cewa an kwato kayan ne a wasu samame daban-daban da aka gudanar bisa bayanan sirri a yankin da rundunar ke kula da shi.
Yusuf ya ce jami’an rundunar na Sansanin Gaba-gaba (FOB) na Amiyi, da ke Atani Abo, sun gano kayan ne a yayin gudanar da sintiri na yau da kullum, inda suka fara ganin alamun haramtattun kayayyakin.
Daga nan ne, jami’an tsaro suka gudanar da cikakken binciken da ya kai su wani rumbun ajiya da ake zargin wanda ake tuhuma da aikata laifin ke amfani da shi wajen boye miyagun kwayoyi.
Ya ce bayan gudanar da bincike mai zurfi a rumbun, jami’an tsaron suka sake gano wasu buhuna dauke da abin da ake zargin tabar wiwi ce.














