Da safiyar yau Laraba 2 ga watan nan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na kasar Masar, Abdel Fattah El-Sisi, a fadar shugaban kasar Masar da ke birnin Alkahira.
Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, a shekara ta 1956, Masar ta kulla dangantakar jakadanci da kasar Sin, wadda ta zama kan gaba tsakanin kasashen Larabawa da na Afirka. Tsoffin shugabannin kasashen biyu sun jagoranci al’ummun kasashen biyu wajen kokarin neman ’yancin kansu, da yaki da mulkin danniya da mulkin mallaka, inda suka kulla zumunci mai karfi.
Xi ya jaddada wasu abubuwa da cewa: na farko, ya dace Sin da Masar su tsaya ga mara wa juna baya, da kiyaye mu’amalar shugabanninsu, da kara tuntubar juna tsakanin bangarori da matakai daban-daban, da inganta musanyar dabaru a bangaren mulkin kasa. Na biyu, ya dace a fadada hadin gwiwa, da habaka mu’amalar juna bisa manyan tsare-tsare. Na uku, ya dace a ci gaba da musanyar al’adu da cudanyar jama’a tsakaninsu. Na hudu, a karfafa hadin gwiwa a bangaren tsaro. Na biyar shi ne, a fadada mu’amalar mabambantan sassa a duniya, da ci gaba da raya dandalin tattaunawa na hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa, da na Sin da kasashen Afirka, da kin yarda da ra’ayin nuna bangaranci da duk wani yunkuri na nuna fin karfi, a wani kokari na kafa tsarin shugabancin duniya mai adalci da daidaito.
Bayan tattaunawarsu, shugabannin biyu sun kuma gane wa idanunsu yadda aka rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyin hadin gwiwa, da suka shafi raya shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, da fasahar kirkirarriyar basira ta AI, da tattalin arziki da cinikayya, da hadin gwiwar tsarin samar da kayayyaki da sauransu.
Sun kuma fitar da wata sanarwar hadin gwiwa game da ci gaba da zurfafa dangantakar abota ta dukkan fannoni kuma bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Masar.Da tsakar ranar yau Laraba kuma, Abdel Fattah El-Sisi gami da mai dakinsa, sun shirya wa shugaba Xi Jinping gami da uwargidansa Peng Liyuan liyafar maraba a fadar shugaban kasar Masar. (Murtala Zhang)














