ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sake Farfado Da Karfin Sojan Japan: Lokaci Ya Yi Da Duniya Za Ta Farka Daga Barcin Rafkana

by Sulaiman
3 weeks ago
Soji

Maitar Japan ta sake farfado da karfin sojinta da ta yi amfani da shi wajen kai hare-hare na zalunci a yakin duniya na biyu ta kara fitowa fili bisa take-taken shugabanni da ’yan ra’ayin rikau na kasar.

Shirin kara yawan kasafin kudin tsaron kasar zuwa tiriliyan 8.9 a kasafin kudin 2027 wanda ba a taba gani ba a tarihin kasar, da yawaitar ziyartar wurin bauta na gaggan masu aikata miyagun laifukan yaki na kasar na Yasukuni a tsakanin jagororin kasar, duk shaidu ne da suka fi rana bayyana kan manufar kasar. Tun a shekarar 2025, kasar Sin take ta kokarin nusar da duniya game da muguwar aniyar Japan amma har yanzu da alama al’ummomin kasa da kasa ba su kai ga farkawa daga barcin rafkana kan lamarin ba.

Amma dai zuwa yanzu, ya kamata a farka, musamman idan aka yi waiwaye game da laifukan yakin da Japan ta aikata a lokacin yakin duniya na biyu. Ko duniya ta manta da kisan kiyashin Nanjing da sojojin Japan suka yi a watan Disamban 1937 tare da aikata fyade da wasu munanan laifuka?

ADVERTISEMENT

Ina batun rukunin soji na 731 wanda hujjojin kotun kasa da kasa da binciken masana suka tabbatar da Japan ta yi amfani da shi wajen yakin amfani da kwayoyin cututtuka tare da gwaje-gwajensu a kan mutane maza da mata yara da manya har ma da jarirai?

Ko an yi biris ne da yadda Japan ta azabtar da fursunonin yaki da yunwa da kisa da sauran nau’ikan azaba musamman bisa misali da fursunonin Australia da Birtaniya 2,500, wanda cibiyar tunawa da tarihin yaki na Australia ta bayyana cewa sojojin kasar guda shida ne kawai suka tsira daga tattaki na tilas tun daga Sandakan zuwa Ranau?

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Shin an manta da badalar “comfort women” ne na sojojin Japan wanda aka samu hujja mai kwari daga ita kanta gwamnatin Japan bisa binciken da ta fitar a shekarar 1993 da ya tabbatar da cewa, rundunar sojan kasar tana da hannu wajen kafawa da gudanar da wuraren na cin zarafin mata?

Dukkan wadannan ba zarge-zargen da aka kirkira bayan shekaru ba ne. An gabatar da shaidu da takardu a gaban kotun soji ta kasa da kasa da aka fi sani da “Tokyo Tribunal”, da shari’ar Khabarovsk ta 1949.

Bugu da kari, binciken masana da aka wallafa a mujallar tarihin kiwon lafiya ta Cambridge ya yi nazari kan tarihin gwaje-gwajen kwayoyin cututtuka a kan mutane da kuma laifukan keta haddi a bangaren kiwon lafiya da Japan ta aikata.

Tarihi ba ya bukatar mu dogara da yanayin abin da muke ji a ranmu, takardu, shaidu, da kotunan yaki da binciken masana sun riga sun samar da hujjoji masu karfi kan ta’asar Japan. Abin da ya rage shi ne, al’ummomin kasa da kasa su farka, su sake bitar hujjojin sannan a dauki kwakkwaran matakin da ya dace. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Soji
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harbawa Da Dawo Da Rokar Zhuque-3 Doron Kasa A Karon Farko

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harbawa Da Dawo Da Rokar Zhuque-3 Doron Kasa A Karon Farko

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.