Kwamitin kolin JKS ya kira taron manema labarai a yau Juma’a, game da ka’idojin jagoranci da aka samu daga zama na 5 na kwamitin kolin na 20.
Tang Fangyu, shugaban ofishin binciken manufofi na kwamitin kolin, ya ce sakatare-janar na kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya taka muhimmiyar rawa yayin tsara kudurin shugabanci na kwamitin game da wasu manyan batutuwa da suka shafi kasancewar jam’iyyar mai juriya da cikakken karfin tsaya da kafarta.
Da yake jinjinawa wannan kuduri a matsayin sakamako mafi muhimmanci na zaman kwamitin kolin na 5, Tang Fangyu ya ce, an tsara kudurin ne karkashin shugabancin kwamitin kolin, inda sakatare-janar Xi Jinping ya jagoranci rukunin tsara daftarin.
A nasa bangare, shugaban sashen tsare-tsare na kwamitin kolin JKS Huang Jianfa, ya ce JKS za ta yi kokarin fadadawa da zurfafa shigar da rassa da ayyukanta cikin sabbin nau’o’in tattalin arziki da kungiyoyin al’umma da kuma rukunoni a sabbin nau’ikan ayyuka, ta yadda sha’awar shiga jam’iyyar za ta kara karfi da tabbatar da dunkulewarta da yin tasiri a bangarori masu tasowa. (Fa’iza Mustapha)














