ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekaru 105 Na Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin: Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa Daga Kwarewar Ci Gaban Kasar Sin

by Sulaiman
2 months ago
Kwaminis

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

A ranar 1 ga watan Yulin 2026, Jam’iyyar Kwaminista Kasar Sin (JKS) za ta cika shekaru 105 da kafuwa, babban lamarin da ya dace a yi waiwaye kan daya daga cikin manyan sauye-sauyen ci gaba da tattalin arziki a tarihin duniya na zamani.
A karkashin jagorancin jam’iyyar, kasar Sin ta sauya daga kasa mai fama da talauci da dogaro da noma zuwa kasa ta biyu mafi girman tattalin arziki a duniya, cibiyar masana’antu ta duniya, kuma jagora a fannonin kimiyya, fasaha da bunkasa ababen more rayuwa.
Nasarorin da kasar ta samu a shekarun baya-bayan nan sun cancanci a yi nazari na musamman a kansu. Duk da rikice-rikicen siyasa da tattalin arziki a duniya da kuma kalubalen cikin gida, tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da bunkasa a lokacin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, inda darajar tattalin arzikinta ya tashi daga sama da yuan tiriliyan 110 a shekarar 2021 zuwa fiye da yuan tiriliyan 140 a shekarar 2025.
Ga kasashe masu tasowa, kwarewar kasar Sin na dauke da muhimman darussa.
Na farko shi ne muhimmancin tsare-tsare na dogon lokaci da kuma dorewar manufofi. Ta hanyar shirye-shiryen raya kasa na shekaru biyar-biyar, kasar Sin ta ci gaba da aiwatar da manufofinta cikin tsari da daidaito ba tare da sauye-sauyen siyasa da ke hana ci gaba ba.
Na biyu shi ne muhimmancin zuba jari a ababen more rayuwa, masana’antu da bunkasa ilimi da kwarewar al’umma. Hanyoyi, layukan dogo, tashoshin jiragen ruwa, makamashi da kuma ilimi sun samar wa kasar Sin ginshikin ci gaban tattalin arziki da inganta rayuwar jama’a.
Na uku kuwa shi ne muhimmancin kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire wajen tafiyar da tattalin arzikin zamani. Ci gaban da kasar Sin ta samu a masana’antun zamani, fasahar zamani da tattalin arzikin dijital ya nuna amfanin saka hannun jari a fannin bincike, ilimi da fasaha.
Haka kuma, abin da ya dace a kara lura da shi, shi ne jajircewar kasar Sin wajen bunkasa ilimi, gina kwarewar ma’aikata da kuma inganta kirkire-kirkire a fannin fasaha. Gagarumar nasarar da kamfanonin kasar Sin suka samu a fannoni kamar kere-keren zamani, na’urorin mutum-mutumi, motocin lantarki, makamashi mai sabuntawa da kuma kwaikwayon fasahar basirar dan Adam (AI) ba ta zo ne kwatsam ba, face sakamakon shekaru da dama na zuba jari mai dorewa a ilimi, binciken kimiyya da kuma koyar da kwarewa.
A wannan karni na ashirin da daya, kasashen da suka yi watsi da kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, dole za su fuskanci hadarin kasancewa a baya a cikin tattalin arzikin duniya dake tattare da gasa.
Har ila yau, nasarar da kasar Sin ta samu wajen rage talauci ta cancanci kulawa ta musamman. Fitar da daruruwan miliyoyin mutane daga kangin talauci cikin shekaru da dama na daga cikin manyan nasarorin da aka taba samu a tarihin ci gaban bil’adama.
Wannan kwarewa ta nuna cewa, ainihin ma’aunin ci gaban tattalin arziki ba wai kawai yana cikin alkaluman tattalin arziki ba ne, amma yana cikin irin ci gaban da ake samu a rayuwar jama’a, walwalarsu da kuma damar da ake samar musu domin inganta rayuwarsu.Ko da yake kowace kasa tana da nata yanayi da kalubale na musamman, manyan darussan da ake iya koya daga nasarar kasar Sin sun hada da hangen nesa na dogon lokaci, shugabanci mai inganci, saka hannun jari a rayuwar mutane da kuma jajircewa wajen cimma manufofin ci gaban kasa.
Yayin da Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin ke bikin cika shekaru 105 da kafuwa, kuma kasar Sin ke fara sabon shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15, kwarewarta na ci gaba da zama wata muhimmiyar hanya ta koyo ga kasashe masu tasowa da ke neman bunkasa tattalin arziki da zamanantar da kasashensu.

Kwaminis
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina Kasa
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
ADC Ta Fara Sayar Da Fom Din Takara Kafin Babban Taron Jam’iyya

2027: ADC Ta Tabbatar Da Karɓar Lambar Shiga Manhajar INEC

LABARAI MASU NASABA

Kwaminis

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.