ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirin “Damammakin Sin Samfurin 2.0”: Tattaki Ne Na Zuwa Sabon Zamani

by Sulaiman
1 month ago

A cikin makonni takwas da suka gabata, fasahar kirkirarriyar basira (AI) ta kasar Sin ta nuna wani kyakkyawan kuzari na samun nasarori tare da samun ci gaba a fannoni daban-daban. Wannan wani babban tsari ne a fili game da salon “kirkire-kirkire da za a iya fadadawa” na kasar Sin inda kirkire-kirkire ba wai kawai za su zamo samun nasara ne a fanni daya tak ba, a’a, amma kafa wani tsari ne na gaba daya mai karfi wanda za a iya sake maimaitawa, da fadadawa, da kuma kimtsa wa amfani da shi a aikace a zahiri.

A yau, salon “kirkire-kirkire da za a iya fadadawa” ya zama babban ginshiki da ke jan hankali a fannin sauye-sauyen masana’antu na duniya. Ana matukar yarda da cewa kasar Sin, ta hanyar amfani da babbar kasuwarta mai matukar fadi, da cikakken tsarin masana’antunta, da ingantaccen tsarin aiwatar da binciken kimiyya a aikace, da kuma tsarin alaka mai bude kofa, ta samar wa duniya da muhimman darussa da fahimta a kan wannan babban buri.Duk da haka, ganin yadda kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin kirkire-kirkire, wasu kasashen yamma sun shiga yanayi na firgici.

Musamman ma wannan ya fi fitowa fili tun daga farkon wannan shekara, inda Amurka ta rika amfani da batun tsaron kasa fiye da kima, sannan a karkashin hujjar kare hakkin mallakar fasaha da tsaron shafin intanet, wajen ci gaba da danniya da dakile kayayyakin manyan fasahohi na zamani na kasar Sin.Sai dai kuma, gaskiyar lamarin ya tabbatar da cewa shirin “Damammakin Sin samfurin 2.0” ya zama babbar matsaya da al’ummomin kasa da kasa suka amince da ita.

ADVERTISEMENT

Kafar yada labarai ta kasar Koriya ta Kudu mai suna Asia News ta ruwaito kwanan nan cewa, babban karfin masana’antu da Sin take da shi, da sabbin nasarorin kirkire-kirkiren fasaha da take samu a-kai-a-kai, da kuma ci gaba da fadada bude kofarta ga duniya, ba wai kawai suna habaka sauye-sauye da daga darajar tattalin arzikinta ba ne, har ma suna samar da sabon sarari ga ci gaban duniya da kuma kulla hadin gwiwa.

Abin da kuma ya fi dacewa a yaba shi ne, a yayin da ake tsaka da samun karuwar gitta shingayen kasuwanci, kasar Sin ta dukufa ga bude kofa da kuma tafiya tare da kowa da kowa, inda take hada hannu da sauran kasashe domin gina tsarin kirkire-kirkire mai samar da moriya ga kowa.Shin kirkire-kirkiren Sin sun haifar da firgici ne ga duniya ko kuwa damammaki? Hujjoji na gaskiya sun riga sun ba da amsar wannan tambaya.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

“Kashe hasken fitilar wani ba ya sa taka fitilar ta fi haske.” Bata suna da danniya daga kasar Amurka da wasu kasashen yammacin duniya ba za su iya hana kasar Sin karfafa ci gaba mai inganci ta hanyar kirkire-kirkire, da kuma zurfafa samar da ci gaba na bai-daya ta hanyar bude kofa ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
NAF Ta Kashe ‘Yan Bindiga Da Dama A Zamfara

Jiragen NAF Sun Kashe Kwamandojin ISWAP, Khalid Al Muhajir Da Wasu Takwas A Borno

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.