Gwamnatin yankin musamman na Macao, ta fitar da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar yankin na shekaru biyar-biyar karo na uku, wanda za a aiwatar tsakanin shekarar nan ta 2026 zuwa 2030.
Shirin wanda ya yi la’akari da ainihin yanayin yankin na Macao, da kuma kudurorin raya kasar Sin baki daya, ya kunshi manyan ginshikai guda hudu, wadanda suka hada da kyautata jagoranci, da sauya salon masana’antu, da bude kofofin yankin, da kuma manufofin kyautata walwalar jama’a. Shirin ya kuma kunshi burikan yankin na mayar da Macao mai bin doka, da Macao mai karsashi, da Macao mai al’adu, da Macao mai walwala, a wani sabon mataki na ingiza ci gaba mai karko karkashin manufar nan ta “Kasa Daya Tsarin Mulki Biyu”.
Sakamakon wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta gabatar, tsakanin masu bayyana ra’ayoyi 1,551 dake Macao, ya nuna yadda kaso 93 bisa dari, suka amince da yadda Macao din ke karbar karin masu yawon bude ido, da kyautatuwar musayar jama’a, da karin jarin waje dake shiga yankin, tun bayan shigarsa hadakar babban yankin Guangdong da Hong Kong da Macao.
A daya bangaren kuma, kaso 92.5 bisa dari na kallon karfin musamman na yankin Macao a matsayin muhimmin fifikonsa, da ya samu daga goyon bayan babban yankin kasar Sin, da kuma rawar da yake takawa a matsayin wata babbar kafa ta kasa da kasa. Har ila yau, kaso 92.2 bisa dari sun jinjinawa nasarar salon Kasa Daya Tsarin Mulki Biyu” da yankin na Macao ke aiwatarwa. (Saminu Alhassan)














