An kaddamar da “Shirin shekaru biyar-biyar na uku na raya ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na Macau (2026-2030)” a ranar Talata da ta wuce, wanda ya tanadi manyan tsare-tsare da shirye-shirye bisa tsari kan ci gaban Macau a shekaru biyar masu zuwa har ma da tsawon lokaci.
Ra’ayoyin jama’a na ganin cewa, shirin na shekaru biyar-biyar na uku ya kasance wani muhimmin mataki da aka kara samun nasarar aiwatar da manufar “Kasa daya, tsarin mulki biyu” mai halayyar musamman na Macau, kuma yana da ma’anar tarihi ta “shiri daya na jagorantar makomar nan gaba” wajen inganta ci gaban Macau mai inganci.
A gefe guda, “Shirin shekaru biyar-biyar na uku” na Macau yana da burin daidaita kansa da “Shirin shekaru biyar-biyar na 15 na kasar Sin”, da dagewa kan daidaita ci gaba da tsaro, tare da himmantuwa wajen shiga tare da ba da hidima ga babban tsarin ci gaban kasa.
A wani gefe kuma, “Shirin shekaru biyar-biyar na uku” ya nuna tare da amfani da fifikon jagorancin zartarwa, watau a karkashin jagorancin gwamnan yankin musamman na Macau ne aka tsara da kuma shirya manyan ayyuka da matakan yin kwaskwarima, tare da nuna yadda aka yi cikakken shawarwari na dimokuradiyya da kuma tattara ra’ayoyin al’umma gaba daya.
A cikin shekaru biyar masu zuwa, yankin Macau zai karfafa hadin gwiwa a fannoni masu yawa da kasashen da suka hada kai wajen raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” da kuma kasashen da ke amfani da harsunan Potrugal da na Sifaniyanci.
Zai kuma mayar da kansa wata muhimmiyar cibiyar bude kofa ga kasashen waje bisa babban mataki, da kuma wata muhimmiyar taga ta musayar wayewar kai da fahimtar juna tsakanin Sin da kasashen yamma. (Bilkisu Xin)














