A yau 20 ga watan Agusta, hukumar kula da harkokin shige da fice ta kasar Sin ta sanarwa da cewa, daga wannan rana, ‘yan kasashen Kyrgyzstan da Vietnam za su iya amfani da manufar izinin yada zango a Sin bisa biza kyauta na sa’o’i 240 da kuma manufar izinin shiga kasar ba tare da biza ba na kwanaki 30 a Hainan.
Ya zuwa yanzu, adadin kasashen da ke amfani da manufar yada zango da biza kyauta na sa’o’i 240 ya karu zuwa 57, kuma adadin kasashen da ke amfani da manufar izinin shiga kasar ba tare da biza ba na kwanaki 30 a Hainan ya karu zuwa 61.
Wani jami’in hukumar kula da harkokin shige da fice ta kasar ya bayyana cewa, aiwatar da wadannan manufofi guda biyu ga ‘yan kasashen Kyrgyzstan da Vietnam, mataki ne dake inganta aikin bude kofa ga ketare a hankali da kuma gina kyakkyawar makomar bil-Adam ta bai daya a yankin da kewayensa, wanda zai taimaka wajen kara kyautata hadin gwiwa tsakanin Sin da sauran kasashe da kuma karfafa sauri da ingancin sha’anin yawon bude ido da ciniki da zuba jari da ziyara. (Amina Xu)














