Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai halarci tarukan gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC a jihohi sama da 20 ba yayin da ake shirin ƙaddamar da kamfen ɗin neman tazarce a ranar 24 ga watan Oktoba, 2026 a birnin Kaduna. A maimakon haka, manyan jiga-jigan jam’iyyar ne za su wakilci shugaban ƙasar a mafi yawan jihohin domin neman goyon bayan masu kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen 2027.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa matakin ya zama dole domin kauce wa barin ɗawainiyar kamfen ta ɗauke masa hankali daga gudanar da ragamar mulkin ƙasa, yana mai jaddada cewa Nijeriya na buƙatar cikakkiyar kulawarsa a ofis a halin yanzu fiye da kowane lokaci. Sai dai ya alƙawarta cewa zai riƙa ware lokaci domin yin jawabi ga ƴan ƙasar kai-tsaye a wasu lokutan, a yayin da kwamitin yaƙin neman zaɓen ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdulaziz Yari ke zagaya sauran jihohi da ƙananan hukumomi.
Wannan sanarwa ta haifar da martani mai zafi daga jam’iyyun adawa, inda Jam’iyyar APM (Allied Peoples Movement) ta danganta rashin halartar shugaban ƙasar da batun yanayin lafiyarsa. Jam’iyyar ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya fito ya zagaya dukkan jihohin ƙasar domin yin kamfen da kansa idan har yana da ƙoshin lafiya, ko kuma ya gaggauta janye aniyarsa ta tsayawa takara a zaɓen mai zuwa.
A nasa ɓangaren, ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ta bakin Daraktan Sadarwarsa Phrank Shaibu, ya bayyana cewa tsoron fuskantar ƴan Nijeriya ne ke hana Tinubu shiga taron gangami saboda gazawar mulkinsa a tsawon shekaru uku da rabi. Atiku ya zargi shugaban da jefa iyalai cikin tsananin yunwa da tsadar rayuwa, yana mai cewa kafin ya nemi sabon wa’adi, wajibi ne ya fuskanci al’umma domin yi musu bayanin abin da ya yi da wa’adinsa na farko maimakon laɓewa a bayan kwamitin kamfe.
Sai dai Shugaban Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Tajudeen Abbas, ya kare matsayin shugaban da jam’iyya mai mulki, inda ya bayyana cewa APC ba za ta ɓoye gaskiyar halin da tattalin arziƙi ke ciki ba. Abbas ya jaddada cewa ko da yake al’umma sun fuskanci ƙalubalen hauhawar farashin kaya, sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya aiwatar sun fara ƙarfafa tushen tattalin arziƙin ƙasar kamar yadda alƙaluman Bankin Duniya suka nuna, kuma jam’iyyar a shirye take ta baje hujjojinta a gaban masu kaɗa ƙuri’a.














