ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaba Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Kaddamar Da Shekarar Cudanyar Al’ummun Sin Da Afirka

by CGTN Hausa and Sulaiman
8 months ago
Xi

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasika mai kunshe da sakon taya murnar kaddamar da shekarar musayar al’adu da cudanyar al’ummu tsakanin Sin da Afirka, a sabuwar shekara ta 2026.

Cikin sakon nasa na jiya Alhamis, shugaba Xi ya ce kaddamar da shekarar a gabar da ake bikin cika shekaru 70, da kaddamar da huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, muhimmiyar matsaya ce da shugabannin sassan biyu suka cimma, ya kuma shaida muhimmin mataki da aka cimma a fannin karfafa goyon bayan al’ummun sassan biyu, ga kawance na Sin da Afirka a sabon mafari na tarihinsu.

Shugaba Xi ya kara da cewa, manyan bangarorin biyu masu dadaddun wayewar kai sun shafe dubban shekaru suna tallafar juna, tare da samar da albarkatu na tarihi da basirar yaukaka kawancen Sin da Afirka.

ADVERTISEMENT

Daga nan sai ya yi kira ga bangarorin biyu, da su yi amfani da wannan zarafi, wajen ingiza kawancen gargajiya, da karfafa koyi da juna tsakanin mabambantan wayewar kai, da fadada musayar al’ummunsu, musamman tsakanin matasa, da zurfafa musayar kwarewa a fannin jagoranci da hadin gwiwar ingiza zamanantarwa.

Ya ce ta wadannan matakai, sassan biyu za su iya ingiza kusancinsu, mai hade da jimillar mutanen Sin da na Afirka su sama da biliyan 2.8, tare da dunkule zukata, da hankula, da karfi, da kuma samar da sabbin gudummawar goyon bayan juna tsakanin kasashe masu tasowa, domin magance kalubalolin duniya, da ingiza akidun bai daya na dan’adamtaka, da gina al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

A jiya Alhamis ne memba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya halarci bikin kaddamar da shekarar musayar al’adu da cudanyar jama’a a tsakanin Sin da Afirka ta shekarar 2026, tare da gabatar da jawabi. A cikin jawabinsa, Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda hudu domin inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Da farko ya ce, ya kamata a fara daga matsayin bukatar neman ci gaba, da hada kai kan aikin inganta zamanantarwa. Kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga kasashen Afirka, ta yadda kasashen nahiyar za su samu karin damammaki a kasuwannin kasar Sin.

Shawara ta biyu ita ce, a tsaya tsayin daka wajen bautawa al’umma, da ba su tallafi. Ya ce, ya dace a mayar da hankali ga zurfafa mu’amala tsakanin jama’ar kasashen Sin da Afirka, domin kara fahimtar dake tsakaninsu.

Kana, shawara ta uku ita ce, a yi musayar fasahohi a aikin gudanar da harkokin kasa da na bangaren siyasa. Kasar Sin tana son zurfafa mu’amalar dake tsakaninta da jam’iyyun siyasa da kungiyoyi daban daban na kasashen Afirka, domin samar da tabbaci ga hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu.

A karshe, Mista Wang ya ce ya kamata a tsaya tsayin daka wajen bude kofa, da nuna fahimta, domin wanzar da abokantaka mai kyakkyawar makomar bai daya. Kasar Sin tana goyon bayan kasashen Afirka, a burinsu na kara taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya, da kuma gyara kurakuran da wasu kasashe suka yi wa kasashen Afirka a baya, domin karfafa ikon su cikin tsarin jagorancin harkokin kasa da kasa.

Baya ga haka, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Congo, mai jan ragamar shugabancin hadin gwiwa na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka, Jean-Claude Gakosso, da shugaban kwamitin kungiyar AU Mahmoud Ali Youssouf, da kuma shugaban kasar Habasha Taye Atske Selassie, su ma sun gabatar da jawabai.

Hakazalika, muhimman wakilai kimanin 200 daga kwamitin kungiyar AU, da sauran hukumomin kungiyar, da ofisoshin jakadancin kasashen Afirka dake kungiyar AU, da hukumomin MDD, da kuma jami’an gwamnatin kasar Habasha, sun halarci wannan biki.

Cikin jawabinsa, Wang Yi ya ce kaddamar da shekarar musayar al’adu da cudanyar jama’a a tsakanin Sin da Afirka, muhimman matakai ne da aka dauka, tun bayan tattaunawa tsakanin shugaba Xi Jinping da shugabannin kasashen Afirka. A halin yanzu, kasashen Sin da Afirka suna cikin muhimmin lokaci na neman bunkasa da farfadowa, kana hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka na da makoma mai haske. Ya kuma kara da cewa, “Ya kamata mu yi amfani da wannan dama ta kaddamar da shekarar musayar al’adu da cudanyar jama’a tsakanin Sin da Afirka, wajen karfafa huldar abota da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, domin kyautata dunkulewar Sin da Afirka a cikin wani sabon zamani, kuma bisa dukkan fannoni, a kokarin tabbatar da kyakkyawar makoma ta dangantakar Sin da Afirka, da kuma bunkasar kasashe masu tasowa.

Shugabannin kasashen Afirka suna ganin cewa, shekarar musayar al’adu da cudanyar jama’a tsakanin Sin da Afirka za ta bude sabon babin dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, da zurfafa mu’amala tsakanin jama’a, ta yadda za a karfafa dankon zumunci a tsakanin bangarorin 2.

An ce, kasashen Afirka suna son yin amfani da wannan dama wajen karfafa hadin gwiwa, da mu’amala a fannonin al’adu, da ba da ilmi, da yawon shakatawa, da fasahohi, tare da zurfafa cudanyar dake tsakanin matasan Sin da Afirka.

Bugu da kari, shugabannin Afirka mahalarta bikin sun ce, kasashen Afirka suna goyon bayan shawarar inganta jagorancin duniya ta (GGI) wadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, kana ya kamata Sin da Afirka su hada kansu wajen adawa da ra’ayin babakere, da kiyaye tsarin duniya mai adalci, gami da kare zaman lafiyar kasa da kasa.

Xi
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Xi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
tallafi

Tasirin Sabbin Manufofin Kudi Na Babban Bankin Nijeriya (CBN)

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.