ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tasirin Sabbin Manufofin Kudi Na Babban Bankin Nijeriya (CBN)

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
6 months ago
tallafi

A wani gagarumin sauyi na manufofi, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bullo da sabbin ka’idojin kula da kudin karba a hannu. Wannan manufa ta fara aiki ne daga 1 ga Janairu, 2026.

A cewar tanade-tanaden wannan manufa, an soke tsoffin iyakokin ajiyar kudi da kuma kudaden ajiya masu wahalarwa, wanda hakan ya ba wa kwastomomin banki damar ajiyar kowane adadin kudi ba tare da biyan ko sisin kwabo ba. Wannan sauyi ne mai kyau da zai kara saukaka harkokin banki ga jama’a.

  • Yawan Fasinjojin Da Jiragen Kasa Suka Yi Jigilarsu a Kasar Sin Ya Zarce Biliyan 4.5 A Shekarar 2025
  • Majalisar Dokokin Legas Ta Amince Da Kasafin Tiriliyan ₦4.4 Na Shekarar 2026

A wannan manufa kuma, an sanya sabuwar iyakar cire kudi na mako-mako wadda ta kai Naira 500,000 ga daidaikun mutane da kuma Naira miliyan 5 ga ‘yan kasuwa da kamfanoni. Haka kuma, manufar ta tanadi cewa duk wanda ya cire kudi fiye da wannan iyaka, dole ne ya biya kudin karin cire kudi, wato kashi 3 cikin 100 ga daidaikun mutane, yayin da kamfanoni za su biya kashi 5 cikin 100.

ADVERTISEMENT

Har ila yau, manufar ta iyanta cire kudi ta na’urar ATM zuwa Naira 100,000 a rana da kuma Naira 500,000 a mako. Haka kuma, cak (chekue) na wani mutum (third-party chekue) da ya haura Naira 100,000 ba za a kara karbarsa a hannu kai tsaye (ober the counter) ba, sai dai ana iya ajiyarsa a asusun banki.

A karkashin wannan sabuwar manufa, CBN ta umurci bankuna da su rika ba ta rahoton duk manyan cire-cire kudi a kowane wata.

LABARAI MASU NASABA

Siyasar 2027: Yadda Ƴan Adawa Ke Ƙara Shiga Tsaka-mai-wuya

Lionel Messi: Mutum Ko Aljan

Sauran tanade-tanaden manufar sun ba bankuna damar rike kashi 60 cikin 100 na kudin karin cire kudi, yayin da CBN ke karbar kashi 40 cikin 100. Ma’anar hakan ita ce bankuna na samun riba idan kwastomomi sun wuce iyakar cire kudi.

Haka kuma, asusun gwamnati da cibiyoyin microfinance kadai aka ware daga wannan doka, domin an soke kebantattun gata da aka bai wa ofisoshin jakadanci, hukumomin diflomasiyya da kungiyoyin tallafi na kasashen waje a baya.

Abin da wannan ke nufi shi ne cewa an kara tsaurara dokokin cire kudi, kuma duk wanda ya wuce iyaka zai biya kudi mai tsada. Sai dai kuma, ajiyar kudi yanzu gaba daya kyauta ce, ba tare da wani caji ba.

Ya kamata a fahimta cewa wannan ba shi ne karo na farko da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke kokarin sarrafa amfani da kudin hannu ba. Wannan tsari ya fara ne tun shekarar 2011, inda babban bankin ke ci gaba da tura manufofi daban-daban domin karfafa tattalin arzikin da ba ya dogaro da kudin hannu (cashless economy). Sai dai wannan sabuwar sanarwar ta fiye dukkan manufofin da suka gabata, kuma ita ce matsakaicin kokari mafi fadi da CBN ta taba yi a wannan fanni.

A cewar masana, manufar wannan doka ita ce: Rage kudin kula da kudin hannu, kamar bugawa, jigilar su da tsaro;

Magance matsalolin tsaro da ke tattare da yawan motsa kudi; – Rage damar yin halastattun kudade; – Da kuma karfafa amfani da hanyoyin biyan kudi na zamani (digital payment systems).

Ya dace a jaddada cewa CBN ba ta da niyyar kawar da amfani da kudin hannu gaba daya, amma tana kokarin sanya manyan mu’amalolin kudin hannu su fi tsada, domin sauya halayyar jama’a zuwa amfani da hanyoyin biyan kudi na zamani.

Ga wadanda ke tunanin za su iya yin dabara, ya kamata su sani cewa iyakar cire kudin tana taruwa ne (cumulatibe). Ba ya damuwa ko mutum ya cire kudi daga bankuna daban-daban ko asusun kudi fiye da daya. CBN na bibiyar dukkan cire-ciren kudi na kowane mutum a dukkan tsarin bankuna. Haka ma abin yake ga ‘yan kasuwa da asusun kamfanoni (corporate accounts).

Bisa tanade-tanaden manufar, cire kudi ta ATM na da nasa iyakar yau da kullum (Naira 100,000 a rana), amma ana kirga wadannan cire-ciren cikin jimillar iyakar mako-mako ta Naira 500,000.

Abin da wannan ke nufi shi ne, idan mutum ya cire Naira 100,000 ta ATM a kowace rana na tsawon kwanaki biyar, to ya riga ya cika duk iyakar cire kudin mako-mako. Duk wani karin cire kudi a wannan makon, ko ta ATM, ko ta POS, ko kai tsaye daga banki, zai haifar da cajin karin cire kudi na kashi 3 cikin 100.

Tasirin wannan manufa ga masu amfani da sabis na banki ya danganta da yadda mutum ke dogaro da kudin hannu.

Abin da ya bayyana karara, bisa tanade-tanaden wannan manufa, shi ne:  Mutane da yawa za su fi dogaro da tura kudi ta banki da hanyoyin biyan kudi na zamani (digital payments);

Samun kudi ta ATM na iya zama mai wahala fiye da da;

Kudaden caji na iya taruwa da sauri idan mutum yana yawan cire kudin hannu;

– Kananan ‘yan kasuwa da ke gudanar da harkokinsu da kudin hannu kawai za su bukaci yin sauyi;

Tsari da shiri za su kara zama dole, kuma manyan kashe-kudi a lokaci guda za su bukaci tsari da shiri tun da wuri.

Ya zuwa yanzu, an fi mayar da hankali ne kan takurawa da iyakoki, duk da cewa abubuwa da dama sun nan yadda suke a baya ko ma sun samu sauki. Daga cikinsu akwai: Ajiyar kudi yanzu gaba daya kyauta ce, domin a baya akwai iyaka da cajin ajiyar kudi;

Canja wurin kudi ta banki (bank transfer) na nan kyauta kuma ba shi da iyaka, babu wata takura kan tura kudi ta hanyoyin dijital;

Biyan kudi ta POS bai samu sauyi ba, domin biyan ‘yan kasuwa ta POS ba ya shiga cikin iyakar cire kudi;

Harkokin banki ta intanet ko wayar hannu suna nan yadda suke, wato biyan kudaden wuta, ruwa, biyan kudin rajista da sauran mu’amalolin dijital ba su canza ba;

Kudin hannu har yanzu halal ne (legal tender), ana iya amfani da su wajen kowace mu’amala, abin da kawai ya canza shi ne an sanya iyaka kan cire manyan adadin kudi.

Masana sun yi amanna cewa cajin karin cire kudi na kashi 3 zuwa 5 cikin 100 ana iya kauce masa, idan kwastomomin banki sun rage dogaro da kudin hannu tare da yin amfani da canja wurin kudi ta banki, POS, ko biyan kudi ta intanet a duk inda ya yiwu; su rarraba cire-ciren kudinsu zuwa makonni daban-daban; su yi amfani da walat din dijital ko canja wurin kudi ta banki wajen kashe-kudin da ke maimaituwa kamar kudin makaranta, haya, rajista, kudin wuta da ruwa, maimakon cire kudi a hannu domin biya.

Yawancin makarantu, masu gidaje da masu ba da sabis yanzu suna karbar biyan kudi ta canja wuri (transfer), kuma ana ba da shawarar a rike kudin gaggawa a tsarin dijital.

Sau da yawa, yanayin gaggawa ne ke tilasta cire manyan kudi lokaci guda, wanda yanzu ke jawo cajin kari. Idan kudin gaggawarka yana cikin asusun ajiya ko jarin da ke ba da damar tura kudi cikin sauri, za ka iya motsa kudin ta hanyoyin dijital ba tare da ketare iyakar cire kudi ba.

Masana sun kuma ba da shawara cewa a rika biyan masu kaya da dillalai ta canja wurin kudi (bank transfer), tare da la’akari da raba hanyar biyan kudi. Misali, idan mutum yana bukatar Naira miliyan 1 don wata mu’amala, zai iya cire Naira 500,000 (ba tare da cajin kari ba) sannan ya shirya canja wurin banki na sauran Naira 500,000.

Sai dai ya kamata a fahimta cewa raba cire kudi zuwa asusu daban-daban ba ya taimako, domin CBN na bibiyar cire-ciren kudi na kowane mutum a dukkan bankuna. Cire Naira 300,000 daga Banki A da Naira 300,000 daga Banki B a mako guda har yanzu jimilla ce ta Naira 600,000, wanda ke jawo caji kan karin Naira 100,000.

A halin da ake ciki yanzu, yana da kyau a rungumi kayan aikin kudi na zamani (digital financial tools). Zai taimaka idan mutum ya tsara kashe-kudinsa ta hanyar dijital ta wannan hanya:

– A rike kudin yau da kullum a walat din dijital ko asusun ajiya;

– A tsara manyan kashe-kudi tun da wuri;

– A sarrafa zirga-zirgar kudi ta atomatik, wato a tsara ajiyar kudi na yau da kullum don kauce wa cire kudi a gaggawa;

– A rage dogaro da ATM, a bar kudi a shirye ta hanyoyin dijital ba tare da ketare iyakar cire kudi ba;

– A gina kyawawan halaye na kudi, domin Nijeriya na komawa tsarin kudin dijital, kuma da wuri mutum ya saba, zai fi kauce wa caji da wahala.

Masana sun kuma ba da shawara cewa a rika biyan masu kaya da dillalai ta canja wurin kudi (bank transfer), tare da la’akari da raba hanyar biyan kudi. Misali, idan mutum yana bukatar Naira miliyan 1 don wata mu’amala, zai iya cire Naira 500,000 (ba tare da cajin kari ba) sannan ya shirya canja wurin banki na sauran Naira 500,000.– A rage dogaro da ATM, a bar kudi a shirye ta hanyoyin dijital ba tare da ketare iyakar cire kudi ba;

A gina kyawawan halaye na kudi, domin Nijeriya na komawa tsarin kudin dijital, kuma da wuri mutum ya saba, zai fi kauce wa caji da wahala.

Nijeriya ba ta kawar da amfani da kudin hannu gaba daya ba, amma alkiblar ta bayyana sarai: amfani da manyan adadin kudin hannu yanzu yana da iyaka, kuma a lokuta da dama yana zuwa da karin kudaden caji.

Gilberts mashawarci ne a kamfanin Magnificat Synergy Nig. Ltd.

CBN
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijar Ta Rattaba Hannu A Kan Dokar Haramta Auren Jinsi
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Za Mu Iya Sayar Da Manmu Ba Tare Da Wata Matsala Ba -Iran
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Dattawan Arewa Sun Buƙaci Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Tabarbarewar Tsaro
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijeriya Ta Karbi Ƴan Nijeriya 268 Da Suka Tsero Daga Afirka Ta Kudu
CBN
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu
  • Sulaiman
    Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani
  • Sulaiman
    Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100
  • Sulaiman
    Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

MASU ALAKA

Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe
Manyan Labarai

Siyasar 2027: Yadda Ƴan Adawa Ke Ƙara Shiga Tsaka-mai-wuya

June 19, 2026
Lionel Messi: Mutum Ko Aljan
Wasanni

Lionel Messi: Mutum Ko Aljan

June 17, 2026
Yari Ya Dace Da Rayuwar Mulki Da Kasuwanci
Nazari

Yari Ya Dace Da Rayuwar Mulki Da Kasuwanci

June 8, 2026
Next Post
Karancin Abinci Mai Gina Jiki Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Yara 469 Cikin Wata 6 A Kano

Karancin Abinci Mai Gina Jiki Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Yara 469 Cikin Wata 6 A Kano

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

June 24, 2026
An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

June 23, 2026
Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

June 23, 2026
Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

June 23, 2026
Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

June 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Mutane 57 Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta’addanci A Adamawa

June 23, 2026
Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

June 23, 2026
Maniyyatan Nijeriya

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Jigilar Alhazan Nijeriya Daga Saudiyya

June 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.