A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta’aziyya ga takwaransa na Indonesia Prabowo Subianto, bisa girgizar kasa mai karfin gaske da ta auku a kasar a ‘yan kwanakin baya.
Da yake bayani game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce shugaba Xi Jinping ya bayyana matukar kaduwarsa, da jin mummunan labarin girgizar kasar da ta auku a Indonesia, wadda ta haddasa asarar rayuka da barnata dukiyoyi.
Ya ce, “A madadin gwamnatin Sin da daukacin al’ummun kasar, ina mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda ibtila’in ya aukawa, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata. Ina fatan karkashin jagorancin gwamnatin Indonesia mai ci, al’ummun kasar za su kai ga shawo kan wannan bala’i, tare da gaggauta sake gina kasarsu”.
Daga nan sai shugaba Xi ya ce, kasarsa na mayar da hankali ga wannan girgizar kasa da ta auku a Indonesia, kuma a shirye take ta samar da tallafi gwargwadon bukatar Indonesia. (Saminu Alhassan)














