ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Akwai Barazanar Ƙaruwar Yunwa A Arewacin Nijeriya – Peter Obi

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya nuna damuwa kan yadda matsalar rashin wadataccen abinci ke ƙara ta’azzara a Arewacin Nijeriya, yana mai cewa lamarin ya zama babban ƙalubale da ke buƙatar matakan gaggawa.

Ya bayyana hakan ne bayan rahoton Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) da ya nuna cewa sama da mutum miliyan 17 a jihohi tara na Arewacin Nijeriya na fuskantar matsananciyar yunwa, yayin da fiye da mutum miliyan 35 a faɗin ƙasar ka iya fuskantar ƙarancin abinci a lokacin daminar ƙarancin abinci.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, Obi ya ce wannan yanayi ya nuna gazawar shugabanci da rashin kyakkyawan tsari, musamman ganin cewa Arewacin Nijeriya ne cibiyar samar da mafi yawan abincin ƙasar.

ADVERTISEMENT

Ya ƙara da cewa rahotanni sun nuna sama da mutum 10,000 sun shiga matsananciyar yunwa mai barazana ga rayuwa, yana mai bayyana hakan a matsayin abin da ke neman gaggawar aikin jin ƙai.

Obi ya danganta matsalar da rashin tsaro, yana cewa hare-haren ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya sun hana manoma komawa gonakinsu tare da tarwatsa al’ummomin manoma a jihohi da dama. Ya ce, “Har sai mun tabbatar da tsaron yankunan noma, ba za mu iya tabbatar da makomar ƙasarmu ba. Rashin tsaro ya hana manoma noma, lamarin da ke barazana ga wadatar abinci a Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

“Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi su mayar da hankali wajen tabbatar da tsaron yankunan noma tare da bai wa ƙananan manoma isasshen tallafi domin ƙara yawan amfanin gona. Haka kuma ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa da Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) da sauran abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa domin cike giɓin tallafin jin ƙai ga waɗanda rikicin ya shafa.

Rahotannin hukumomin agaji sun nuna cewa rikice-rikice, da ƙauracewa daga muhallai da raguwar tallafin jin ƙai na tura Arewacin Nijeriya zuwa mafi munin matsalar yunwa cikin kusan shekaru goma, inda miliyoyin mutane ke fuskantar matsananciyar rashin wadataccen abinci.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Babban Dan Majalissar Dokokin Kasar Sin Ya Halarci Jana’izar Marigayi Jagoran Addini Na Iran

Babban Dan Majalissar Dokokin Kasar Sin Ya Halarci Jana’izar Marigayi Jagoran Addini Na Iran

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.