ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Gidauniyar Ɗahiru Mangal Ta Tallafa Wa Marasa Lafiya 30,000 A Katsina

by El-Zaharadeen Umar
2 months ago

Gidauniyar Ɗahiru Bara’u Mangal ta bayyana cewa marasa lafiya masu ƙaramin ƙarfi sama da 30,000 ne suka amfana da shirye-shiryen ba da magani kyauta da ya gudanar a faɗin Jihar Katsina tun daga shekarar 2018.

Haka kuma, gidauniyar ta fara tantancewa da kula da kusan marasa lafiya 2,000 masu fama da cututtukan ido daban-daban, ciki har da waɗanda ke buƙatar tiyata.

Mamba a kwamitin amintattu na gidauniyar, Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin yi wa marasa lafiya sama da 700 tiyatar ƙumburin mara (Hernia) da kuma Hydrocele kyauta a babban asibitin Katsina.

ADVERTISEMENT

Kabir ya ce marasa lafiya sama da 700 daga sassa daban-daban na Jihar Katsina da ma wasu jihohi ne ake sa ran za su amfana da shirin tiyatar kyauta.

Ya bayyana cewa manufar shirin ita ce ƙara sauƙaƙa wa marasa ƙarfi samun ingantaccen kulawar lafiya.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A cewarsa, ana fara tantance marasa lafiyar kafin a yi musu tiyata kyauta, yayin da waɗanda ke fama da ƙananan cututtuka za a ba su magunguna ba tare da sun biya komai ba.

“Shirin ana gudanar da shi lokaci-lokaci, kuma Alhaji Ɗahiru Bara’u Mangal ne ke ɗaukar nauyin komai domin samar da ingantaccen kulawar lafiya ga marasa galihu.

“Duk marasa lafiyar da ke buƙatar tiyata za a yi musu kyauta, yayin da waɗanda ke da ƙananan matsalolin lafiya za a ba su magungunan da suka dace ba tare da wani kuɗi ba,” in ji shi.

Kabir ya ƙara da cewa gidauniyar na kuma ɗaukar nauyin tiyatar ido kyauta, tiyatar cututtukan mafitsara da hanyoyin fitsari (urology), da sauran ayyukan jinya na musamman a faɗin Jihar Katsina. 

Shi ma da yake jawabi, Dakta Saifullahi Bawale ya yaba wa gidauniyar bisa yadda take taimaka wa gwamnati wajen inganta harkokin kiwon lafiya ta hanyar shirye-shiryen jinya kyauta.

Ya ce shirin ya dawo da fata ga dubban marasa ƙarfi da ba su da ikon biyan kuɗin magani.

A cewarsa, an tanadi isassun likitoci, ma’aikatan lafiya, kayan aiki, magunguna da sauran kayayyakin da ake buƙata domin tabbatar da nasarar shirin.

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da shirin sun gode wa gidauniyar, suna cewa tallafin ya sake ba su fata.

Malama Zulaihat Adamu daga ƙaramar hukumar Jibiya ta bayyana farin cikinta cewa ɗanta zai samu tiyatar Hernia kyauta, tana mai cewa sun daɗe ba su da ƙarfin biyan kuɗin maganin.

Shi ma Shamsu Abubakar ya yaba wa gidauniyar bisa ɗaukar nauyin tiyatar idonsa, tare da addu’ar Allah ya sa wannan ya zama ƙarshen matsalar idon da yake fama da ita.

Firdausi Muhammad daga ƙaramar hukumar Batsari ta ce shirin babban sauki ne ga marasa lafiya da ba za su iya biyan kuɗin tiyata ba, tare da yi wa wanda ya kafa gidauniyar addu’ar Allah ya ƙara masa albarka.

Rahotanni sun bayyana cewa gidauniyar na ci gaba da gudanar da shirin kula da lafiyar ido kyauta a cibiyar kula da Ido ta Katsina, inda ake tantancewa da ba marasa lafiya magani ba tare da biyan kuɗi ba.

Haka kuma, ana ba marasa lafiyar da ke buƙatar tabarau kyauta, yayin da waɗanda aka gano suna buƙatar tiyatar ido ake tsara musu ranar yin tiyatar ba tare da wani kuɗi ba.

El-Zaharadeen Umar
+ postsBio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Tawaga Ta Biyu Ta Kwararrun Kasar Sin Ta Sauka A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Domin Karfafa Yaki Da Cutar Ebola

Tawaga Ta Biyu Ta Kwararrun Kasar Sin Ta Sauka A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Domin Karfafa Yaki Da Cutar Ebola

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.