A yayin taron hadin gwiwar kafafen yada labarai na Sin da kasashen Afirka karo na 7 da ya gudana jiya Alhamis a birnin Beijing, kwararru mahalarta zaman sun ce Sin da kasashen Afirka na karfafa hadin gwiwa a fannin fasahohin AI da jagoranci, da nufin cimma nasara tare a fannin watsa shirye-shirye ta amfani da fasahohin kirkire-kirkire.
Da yake tsokaci yayin taro, babban daraktan cibiyar watsa shirye-shirye ta Afirka ko AUB Gregoire Ndjaka, ya ce a halin yanzu masana’antar yada labarai ta fara shiga wani sabon karni. Inda fasahar AI, da sauyin harkokin dijital, da sabbin dandalolin watsa bayanai, da sauyin halayyar masu karbar sakwanni ke canza fasalin yadda ake samar da abubuwa, da rarraba su, da yadda ake karbarsu.
A nasa jawabin kuwa, ministan watsa labarai na kasar Saliyo Chernor Abduli Bah, cewa ya yi kasarsa na fatan kara bunkasa hadin gwiwar fasahohin yada labarai tare da kasar Sin. Kasar Sin ta riga ta samu kwarewa mai nagarta, da sanin makamar aiki cikin shekaru da dama.
Ya ce “Ba batun mu ci gajiyar fasahohin Sin kadai ba ne. Burinmu shi ne mu shiga a dama da mu a fannin kirkirar sassan ayyukan AI, da fasahohin fannin, ta yadda wadannan sassan aiki na AI za su zamo masu biyan bukatun mu.” (Saminu Alhassan)














