Majalisar gudanarwar kasar Sin, ta fitar da shirin gaggauta raya harkokin noma da zamanantar da karkara, wanda za a aiwatar karkashin shirin raya kasa karo na 15 tsakanin shekarar nan ta 2026 zuwa 2030.
Shirin na da nufin amfani da bunkasa noma, da zamanantar da karkara wajen cimma nasarar zamanantar da kasar ta Sin, ya kuma kunshi muhimman sassa, da matakai masu nasaba, wadanda za su taimaka wajen cimma burin da aka sanya gaba.
Kazalika, shirin na da burin kara kyautata ikon kasar Sin na dogaro da kai, da karfin tasiri a fannonin kimiyya da fasahar noma, da kara azamar sauya akalar harkar noma zuwa babbar masana’antar zamani, da ci gaba da fadada kudaden shigar manoma cikin gaggawa nan zuwa shekarar 2030. (Mai fassara: Saminu Alhassan)















Discussion about this post