Kasar Sin ta kudurta kara yawan wutar lantarkin da take samarwa daga sassan makamashi mai tsafta zuwa kashi 50% nan da shekarar 2030, kamar yadda wani sabon shiri na kasa da aka fitar ya bayyana, wanda ya fayyace tsarin bunkasa bangaren samar da wutar lantarki na kasar a tsakanin 2026 zuwa 2030.
Shirin na shekaru biyar, wanda hukumar kula da ci gaban kasa da gyare-gyare da hukumar kula da makamashi ta kasa suka fitar cikin hadin gwiwa, ya shimfida tsarin gudanarwa da za a yi aiki da shi a bangaren samar da wutar lantarki na kasar a tsakanin shekarar 2026 zuwa 2030, tare da kudurta kafa sabon tsarin samar da wutar lantarki nan da shekarar 2030.
A karkashin wannan shiri, kasar Sin ta kuduri aniyar sada sabbin hanyoyin samar da makamashi masu karfin da ya haura kilowat biliyan 2.8 da tsarin layukan bayar da wutar lantarki na kasa, tare da gina cibiyoyin caji masu karfin yi wa motocin lantarki sama da miliyan 110 caji nan da shekarar 2030.
Domin cimma wadannan kudurori, shirin ya tsara wasu abubuwa da za a ba da fifiko, ciki har da fadada samar da wutar lantarki mara gurbata muhalli da mai karancin fitar da hayakin carbon, da gina ingantaccen tsarin layukan bayar da wutar lantarki mai juriya, da habaka tsarin wutar lantarki mai saukin lamari, da bunkasa samar da wadatacciyar wutar lantarki, da zurfafa gyare-gyaren wutar lantarki ta fuskar kasuwanci, da kuma karfafa hadin gwiwa da kasashen duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














