An yi bikin aza harsashin ginin cibiyar tiyata ta kasar Mozambique da Sin za ta taimaka wajen ginawa, a jiya Litinin a Maputo, babban birnin kasar.
Shugaban Mozambique Daniel Francisco Chapo wanda ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi, ya bayyana cewa, wannan aiki zai zama wata kyakkyawar shaida game da hadin gwiwar kiwon lafiyar jama’a tsakanin Mozambique da Sin.
Chapo ya kara da cewa, Mozambique da Sin sun kulla kawance mai karfi na tsawon shekaru da dama, bisa mutunta juna da amincewar siyasa. Aikin cibiyar tiyata ta kasar da Sin za ta taimaka wajen ginawa zai kawo jin dadin dubban iyalan Mozambique, kuma karin al’ummar Mozambique za su sami damar samun ayyukan kiwon lafiya na musamman a kasar. (Amina Xu)














