Kasar Sin ta lashe lambar zinari daya da ta azurfa uku a gasar kimiyyar nukiliya ta duniya (INSO) karo na uku da aka gudanar a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, jiya Asabar, wanda ya kasance karo na farko da kasar ta shiga gasar.
Tawagar kasar Sin mai mambobi hudu ta kasance daya daga cikin manyan mahalarta da suka sami sakamako mafi kyau a gasar. Gasar ta tsawon kwanaki takwas ta hallara tawagogi daga kasashe 19, inda aka gudanar da jarrabawa kan ka’ida da kuma gwaje-gwaje a fannoni daban-daban, da suka hada da kimiyyar ilimin fisik na nukiliya, da kariya daga yanayin fitar makamashi ko radiation a turance, da kuma man nukiliya.
Wakilin kwamitin tsara gasar, Talal Alrashidi, ya yi maraba da shigar kasar Sin cikin gasar, inda ya bayyana cewa daliban sun nuna kwazo mai ban sha’awa sannan sun nuna kyakkyawan ruhin matasan Sinawa.Wanda ya lashe lambar zinari, Liu Siqi, dalibin makarantar sakandare ta Beijing mai lamba 80 reshen Wangjing, ya bayyana cewa fafatawa tare da hazikan matasa daga ko’ina cikin duniya ta “kara mani kwarin gwiwa da kudurin yin karatu tukuru da kuma cimma sababbin nasarori a matakin koli a fannin kimiyya.”
Gasar ta INSO, wadda aka kaddamar a shekarar 2024 tare da goyon bayan hukumar makamashin nukiliya ta duniya (IAEA), ita ce gasa ta farko ta matasa ta duniya da aka sadaukar domin kimiyyar nukiliya, da nufin karfafa sha’awar matasa a fannin gami da habaka musaya a tsakanin kasa da kasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














